Yadda wani bawan Allah ya kubutar da jirgi samfurin Lion 737 daga hadari

Yadda wani bawan Allah ya kubutar da jirgi samfurin Lion 737 daga hadari

Tabbas dai tsautsayi baya wuce ranar sa, kuma dukkan mai rai baya tsallake ranar ajalin sa. Hakan dai ta sake tabbata a wani labarin da muka samu na wani bawan Allah da ya kubutar da jirgin sama samfurin Boeing Co.737 Max 8 daga yin hatsari.

Wannan dai kamar yadda muka samu ya auku ne a rana daya kafin aukuwar mummunan hatsarin jirgin saman nan irin samfurin mallakin kasar Itofiya ta dalilin tangardar da ake tunanin suna da kamanceceniya.

Yadda wani bawan Allah ya kubutar da jirgi samfurin Lion 737 daga hadari
Yadda wani bawan Allah ya kubutar da jirgi samfurin Lion 737 daga hadari
Asali: UGC

KU KARANTA: Hukumar 'yan sanda ta daura damarar yaki da masu tada zaune tsaye a Filato

Kamar dai yadda mu kasamu, mutumin da ya Allah ya taimaka ya kubutar da jirgin dai an ce shima matukin jirgi ne sai dai a ranar ba shi ke tuka jirgin ba kuma yana ganin alamun jirgin da yake ciki ya samu matsalar sai ya je wurin matuka jiragen ya kuma bayyana masu yadda za su magance matsalar.

To sai dai kaddara ta riga fata domin kuwa wanshekare ne wani jirgin irin samfurin ya gamu da irin cikas din kuma har ma ya yi hatsari tare da kashe dukkan mutanen da ke cikin sa su 189 ta dalilin irin matsalar.

Shi dai kamfanin dake kera jirgin samfurin Boeing Co. 737 Max 8 yanzu haka yana kan fuskantar matsin lamba mai girma sakamakon matsalolin da jirgin ke samu da har hakan ta yi sanadiyyar faduwar jirage biyu a kwana-kwanan nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel