Yanzunnan: Yan kungiyar asiri sun katse rayuwar dalibi da masu bautar kasa 2 a Bayelsa

Yanzunnan: Yan kungiyar asiri sun katse rayuwar dalibi da masu bautar kasa 2 a Bayelsa

Wasu da ake kyautata zaton cewa 'yan kungiyar asiri ne sun kashe wasu mata masu yiwa kasa hidima (NYSC) guda biyu tare da wani dalibi a wata makarantar 'yan kasuwa da ke Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan kungiyar asirin sun dade suna kashewa tare da yiwa al'ummar da ke zaune a garin fashi da makami, karkashin wani yanayi da ake ganin kamar ya zarce karfin ikon rundunar 'yan sanda da sauran jami'an tsaro.

Cikakken labarin yana zuwa...

KARANTA WANNAN: Da zafinsa: 'Ku zabi Ganduje a Kano - Takai ya bukaci magoya bayansa

Yanzunnan: Yan kungiyar asiri sun katse rayuwar dalibi da 'yan sanda 2 a Bayelsa
Yanzunnan: Yan kungiyar asiri sun katse rayuwar dalibi da 'yan sanda 2 a Bayelsa
Asali: Depositphotos

A wani labarin kuwa; dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyyar PRP, Mallam Salihu Sagir Takai ya umarci magoya bayan sa da su zabi gwamnan jihar mai ci a yanzu, Dr Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyar APC a zaben karashe na gwamna da za'a gudanar ranar asabar, 23 ga watan Maris, 2019.

Mallam Takai ya sanar da haka ne yayin da yake ganawa da magoya bayan sa a Kano, inda ya shaida masu cewa "Ganduje ya neme ni, mun kuma tattauna tare da cimma matsayar cewa hadaka a tsakaninmu ce kawai za ta kawo ci gaba a jihar Kano."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel