Ko sama ko kasa an nemi Atiku da gwamnoni an rasa a taron gaggawa da PDP ta kira

Ko sama ko kasa an nemi Atiku da gwamnoni an rasa a taron gaggawa da PDP ta kira

Dan takarar Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar da dukkanin zababbun gwamnoni a inuwar jam’iyyar, a jiya basu halarci taron gaggawa da iyayen jam’iyya suka gudanar ba a Abuja.

Daga yankin Arewa maso gabas, ba a ga Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba ba da kuma Dankwambo na jihar Gombe.

Daga yankin Arewa ta yamma, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto da bai hallara ba, yayinda daga Arewa ta tsakiya kuma, aka nemi Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, da takwaransa na jihar Kwara, Ahmed Abdulfattah aka rasa.

Ko sama ko kasa an nemi Atiku da gwamnoni an rasa a taron gaggawa da PDP ta kira
Ko sama ko kasa an nemi Atiku da gwamnoni an rasa a taron gaggawa da PDP ta kira
Asali: Facebook

Hakazalika daga kudu maso kudu, ba a ga Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ba, da kuma Ifeanyi Okowa na Delta, Ben Ayade na Cross River; Emmanuel Uddom na Akwa Ino; da kuma Seriake Dickson na jihar Bayelsa.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Abunda ya faru cuta ce karara - Dogara

A kudu maso gabas, ba a ga Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi da takwaransa Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu ba, da kuma Ikezie Ikpeazu na jihar Abia.

Sai dai, Shugaban PDP na kasa, Prince Uche Secondus yace, Atiku da gwamnonin basu hallara ba saboda suna shirye-shiryen zaben da za a sake gudanarwa a ranar Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel