Uwargidata dukan tsiya take min koda yaushe - Wani Miji ya bayyanawa koyu

Uwargidata dukan tsiya take min koda yaushe - Wani Miji ya bayyanawa koyu

Wani dan kasuwa a garin Ibadan mai suna Oluwatosin Baare, a ranar Laraba ya bayyanawa kotu dake zaune Mapo, Ibadan cewa yana bukatar kotu ta raba aurensa da matarsa, Enitam, saboda tana yawan dukansa.

Yace: "Kuskuren da nayi shine rashin gudanar da bincike mai zurfi kafin auren Enitan, shine babban matsalana a yau. Tun lokacin da Enitan ta shigo gidana ta canza, tana yawan kalubalantar umarnina."

"Na yi iyakan kokarina wajen ganin cewa na gyara halayyanta ta hanyar sanar da Fastonmu, amma abun kara tsanani yakeyi."

A watan oktoba, 2018, Enitan ta shigo daki ta waska min mari sannan ta dauko wuka cewa zata soka min. Da kyar da sullube mata."

KU KARANTA: Akwai abin tarihu guda daya da zan kafa a Najeriya – Buhari

"Ba zan iya kirga lokutan da ta yaga min kaya a coci ba da kuma bainar jama'a. Wni zubin idan na dade a wajen aiki, Enitan zata bugeni idan na dawo."

"A ranar 16 ga watan Nuwamba, Enitan ta caka min 'Chisel' a coci. Na daina kai karanta wajen iyayenta saboda na lura babu wani mataki da suke shirin dauka."

"Tun lokacin da na auri Enitan shekar bakwai da suka gabata, bata samu juna biyu ba. Babu wani soyayya tsakanina da Ita, saboda haka a rabamu."

Uwargidar dai ta ce sam bata amince a raba auren ba, duk da cewa bata musa tuhume-tuhumen da yayi mata ba.

Ya kuke ganin za'a kare?

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel