Jihar Bauchi: PDP ta lashe zaben kujerar dan majalisar dokokin Tafawa Balewa

Jihar Bauchi: PDP ta lashe zaben kujerar dan majalisar dokokin Tafawa Balewa

- Jam'iyyar PDP ta lashe zaben kujerar mazabar karamar hukumar Tafawa Balewa a majalisar dokokin jihar Bauchi

- PDP ta lashe zaben da kuri'u 29,933 yayin da jam'iyyar APC ta samu kuri'u 25,210

- Jam'iyyar PDP ta lashe zaben ne bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dawo ci gaba da karbar sakamakon zaben karamar hukumar

Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyar PDP ta samu nasarar lallasa jam'iyyar APC a kujerar majalisar dokoki ta karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar, inda PDP ta samu kuri'u 29,933 yayin da jam'iyyar APC ta samu kuri'u 25,210.

Sai dai har yanzu ba a tattara sakamakon zaben gwamnan jihar ba bayan da wata babbar kotun gwamnatin tarayya ta saurari wani korafi da gwamnan jihar Mohammad Abubakar tare da jam'iyyar APC suka shigar na kin amincewa da ci gaba da karbar sakamakon zaben.

KARANTA WANNAN: Inna Lillahi wa inna ilayhi raji'un: Wani gari ya kone kurmus a gobarar Jigawa

Jihar Bauchi: PDP ta lashe zaben kujerar dan majalisar dokokin Tafawa Balewa
Jihar Bauchi: PDP ta lashe zaben kujerar dan majalisar dokokin Tafawa Balewa
Asali: UGC

Idan za a iya tunawa, baturen zaben jihar Bauchi, Farfesa Mohammed Kyari ya soke zaben karamar hukumar Tafawa Balewa bayan da hukumar zaben ta samu korafin cewa an yi hargitis a cibiyar tattara sakamakon zaben karamar hukumar.

Wani kwamiti da INEC ta tura Bauchi, bisa jagorancin Festus Okoye, ya bukaci hukumar da ta ci gaba da karbar sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa.

Sai dai hukumar ta dawo da ci gaba da karbar sakamakon zaben kujerar majalisar dokoki, amma ta dakatar da karbar sakamakon zaben gwamnan jihar bisa bin umurnin kotu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel