Inna Lillahi wa inna ilayhi raji'un: Wani gari ya kone kurmus a gobarar Jigawa

Inna Lillahi wa inna ilayhi raji'un: Wani gari ya kone kurmus a gobarar Jigawa

- Hukumar bada agajin gaggawa ta tabbatar da cewa wata gagarumar gobara ta lalata gidaje a kauyen Barebari a karamar hukumar Ringim na jihar Jigawa

- Hukumar ta ce har zuwa yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar da ta fara da misalin karfe 11 na safiya har zuwa karfe shida na yamma a ranar Talata ba

- Gobarar ta lalata kusan gaba daya kauyen da suka hada da dabbobi da kayan abinci. Sama da gidaje 60 ne gobarar ta lakume

Sani Yusuf, babban sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Jigawa, ya tabbatar da cewa wata gagarumar gobara ta lalata gidaje a kauyen Barebari a karamar hukumar Ringim na jihar Jigawa.

Yusuf ya ce har zuwa yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar da ta fara da misalin karfe 11 na safiya har zuwa karfe shida na yamma a ranar Talata ba.

Ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Laraba a garin Dutse cewa gobarar ta lalata kusan gaba daya kauyen.

KARANTA WANNAN: Zaben shugaban kasa 2015: Jonathan ne ya kashe kansa na kin zuwa kotu - Buba Galadima

Inna Lillahi wa inna ilayhi raji'un: Wani gari ya kone kurmus a gobarar Jigawa
Inna Lillahi wa inna ilayhi raji'un: Wani gari ya kone kurmus a gobarar Jigawa
Asali: Twitter

"Gobarar ta lalata kusan gaba daya kauyen da suka hada da dabbobi da kayan abinci. Sama da gidaje 60 ne gobarar ta lakume. Gobarar ta fara da misalin 11 har zuwa karfe 6 ta na ci.

" Duk da cewa ba mu cika damuwa da yawan gidajen ba, dabbobi da kayan abinci da suka lalace ba, amma yadda zamu taimakawa wadanda gobarar ta shafa saboda shi ne muke kan tattaunawa yanzu. Muna shirin samar masu da kayan jin kai, da suka hada da muhalli da abinci.

"Bayan mun yi haka ne za mu fara bin diddigin dalilin barkewar gobarar da kuma iya barnar da ta yi," a cewarsa.

Babban sakataren ya kara da cewa za a kai masu tallafin ne da nufin saukaka masu kan wahalhalun da suke fuskanta.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Khadijah Thabit avatar

Khadijah Thabit (Copyeditor) Khadijah Thabit is an editor with over 3 years of experience editing and managing contents such as articles, blogs, newsletters and social leads. She has a BA in English and Literary Studies from the University of Ibadan, Nigeria. Khadijah joined Legit.ng in September 2020 as a copyeditor and proofreader for the Human Interest, Current Affairs, Business, Sports and PR desks. As a grammar police, she develops her skills by reading novels and dictionaries. Email: khadeeejathabit@gmail.com