Kano: Na riga na kafa majalisar Abba gida-gida - Kwankwaso

Kano: Na riga na kafa majalisar Abba gida-gida - Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Shugaban jam’ iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yace ya riga ya kafa majalisar dan takarar gwamna a PDP, Abba Kabir Yusuf.

Ya bayyana cewa lallai wadanda ke masa biyayya da tafiyar Kwankwasiyya ne kadai za su kasance a cikinta.

Kwankwaso ya kara da cewa tuni jerin sunayen yan majalisar Abba na a hannunsa sannan cewa zai sanar dasu kasa da mako biyu bayan rantsarwa a ranar 29 ga watan Mayu 2019.

Kwankwaso, wanda ya kasance surukin Abba, ya bayyana cewa yayi amfani da ikon sa don ganin Abba yayi nasara a zaben da za a sake a jihar.

Kano: Na riga na kafa majalisar Abba gida-gida - Kwankwaso
Kano: Na riga na kafa majalisar Abba gida-gida - Kwankwaso
Asali: UGC

Da yake Magana a Kano, tsohon ministan tsaron yace: “A matsayina na Shugaban PDP a Kano, Ina da damar zabar wadanda ke biyayya a gare ni kawai da kuma yan tafiyar Kwankwasiyya domin tafiyar da gwamnatinmu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Motar makaranta dauke da yara sama da 40 yayi hatsari a Ekiti

“Na riga na yanke hukunci akan haka saboda bana son sake maimaita abunda ya faru dani a gwamnatin Ganduje.

“Tuni na mallaki jerin sunayen wadanda ke biyayya ga Kwankwasiyya sannan kuma za a sanar da su kasa da makonni biyu bayan rantsar da sabon gwamna.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel