Kaduna: Yadda jarirai 6,000 za su kamu da cutar kanjamau a 2019 - UNICEF

Kaduna: Yadda jarirai 6,000 za su kamu da cutar kanjamau a 2019 - UNICEF

- UNICEF ta ce akalla jarirai 6,000 ne a jihar Kaduna za su iya kamuwa da cutar kanjamau a shekarar 2019 idan har ba a dakile yaduwar cutar daga uwa zuwa jariri ba

- Kaduna na daya daga cikin jihohi hudu a kasar wacce UNICEF ke tallafamawa da shirin eMTCT har zuwa 2020 da nufin kawo karshen yaduwar AIDs kafin shekarar 2030

- Ya kuma ce jihar na kokowa da karancin wayar da kan jama'a dangane da muhimmancin shirin eMTCT da kuma karancin kayayaki

Gidauniyar tallafawa kananan yara cikin gaggawa ta majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta ce akalla jarirai 6,000 ne a jihar Kaduna za su iya kamuwa da cutar kanjamau a shekarar 2019 idan har ba a dakile yaduwar cutar HIV daga uwa zuwa jariri ba.

Zakari Adam, babban jami'in UNICEF a jihar Kaduna, ya bayyana hakan a wani taron kwana daya da ya gudana a ranar Litinin.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa taron ya gudana ne ga matan kanan hukumomi a jihar domin wayar masu da kai dangane da kaddamar da shirin dakile yaduwar cutar kanjamau daga uwa zuwa jariransu da aka assasa a 2018.

KARANTA WANNAN: Ya zama wajibi INEC ta sanar da 'yan Nigeria gaskiya kan zaben jihar Bauchi - APC

Kaduna: Yadda kananan yara 6,000 za su kamu da cutar kanjamau a 2019 - UNICEF
Kaduna: Yadda kananan yara 6,000 za su kamu da cutar kanjamau a 2019 - UNICEF
Asali: UGC

Mr Adam ya ce jihar Kaduna na daya daga cikin jihohi hudu a kasar wacce UNICEF ke tallafamawa da shirin eMTCT har zuwa 2020 da kuma kawo karshen yaduwar AIDs kafin shekarar 2030.

Ya ce duk da cewa jihar ta samu nasarar cimma shirin eMTCT daga kashi 16 a 2012 zuwa kashi 66 a 2017, har yanzu suna samun fuskantar kalubale wajen kula da mata masu dauke da juna biyu a shirin ANC da kuma wajen haihuwa a asibiti.

Ya kuma ce jihar na kokowa da karancin wayar da kan jama'a dangane da muhimmancin shirin eMTCT da kuma karancin kayayakin aiki da zai samar da ingantaccen kiwon lafiya a jihar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel