Allah ya kare: Mummunar gobara ta yi barna a garin Bogocho

Allah ya kare: Mummunar gobara ta yi barna a garin Bogocho

Da yammacin yau ne aka samu aukuwar wata mummunar gobara a gabar da kasuwa cikin gidan Alhaji Hassan Bogocho, kamar dai yadda wani ma'abocin anfani da kafar sadarwar zamani ta Fezbuk ya wallafa hotunan gobarar a shafin sa.

Matsalar tashin gobara dai na daga cikin ibtila'o'in da suka addabi al'umma musamman ma a Arewacin Najeriya da hakan auku lokaci zuwa lokaci kuma akan samu asarar dukiya wani lokacin ma hadda rayuka.

Allah ya kare: Mummunar gobara ta yi barna a garin Bogocho
Allah ya kare: Mummunar gobara ta yi barna a garin Bogocho
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zaben Adamawa: INEC ta fitar da sabbin bayanai

A watan Disembar da ya gabata ma dai, da misalin karfe biyu saura na daren Juma'a ne wata gobara ta tashi har zuwa wayewar gari a babbar kasuwar keffi dake jihar Nasarawa.

Gobarar ta kone kayyaki na milyoyin nairori. Wata majiya ta ce har yanzu ba a san musabbabin gobarar ba.

Amma ya ce bala'in gobara a kasuwar ta Keffi ya zama wani abin al'ajibi domin duk shekara a daidai irin wannan lokaci sai wuta ta tashi a kasuwar.

Shugaban karamar hukumar Keffi Alhaji Abdurrahman Sani Maigoro ya shaida mana cewar lokacin da suka sami labarin faruwar lamarin sun yi kokarin kiran jami'an kashe gobara na Keffi ba su samu zuwa ba, don haka bai yi kasa a gwiwa ba sai da ya kira ofishin kashe gobara na Abuja amma suka ba shi wasu dalilai na rashin tsaro, haka dai wutar ta cinye dukiya mai tarin yawa.

Muna Addu'ah Allah ya maida masu da mafificin abun da suka rasa, Amin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel