Sabon zabe: Hukumar INEC ta fitar da sabbin bayanai akan zaben gwamnan Adamawa

Sabon zabe: Hukumar INEC ta fitar da sabbin bayanai akan zaben gwamnan Adamawa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) ta ta fitar da sabbin bayanai game da zaben da za'a sake yi a jihar Adamawa ranar 23 ga watan Maris, watau ranar Asabar mai zuwa.

Hukumar ta INEC dai ta bayyana cewa za'a sake gudanar da zabukan ne a akalla kananan hukumomi 14, mazabu 29 kuma rumfunan zabe 44 da ke da mutanen da suka yi rijista sama da dubu arba'in.

Sabon zabe: Hukumar INEC ta fitar da sabbin bayanai akan zaben gwamnan Adamawa
Sabon zabe: Hukumar INEC ta fitar da sabbin bayanai akan zaben gwamnan Adamawa
Asali: UGC

KU KARANTA: Zaben Ribas: APC ta karyata hukumar INEC

Babban kwamishin hukumar ta Independent National Electoral Commission (INEC) a jihar Adamawa, Kasim Gaidam ne ya bayyanawa manema labarai hakan a ofishin sa dake a garin Yola, babban birnin jihar ta Adamawa.

A cewar sa, hukumar kawo yanzu ta kammala dukkan shirye-shiryen ta don gudanar da zaben tare kuma da bayar da tabbacin yi wa kowa adalci a yayin zaben.

A cewar sa, kananan hukumomin da za'a sake zaben a jihar sun hada da Yola ta kudu, Fufore, Ganye, Girei, Guyuk da kuma Hong.

Sauran haka zalika sun hada da Lamurde, Numan, Madagali, Michika, Mubi North, Shelleng, Song da kuma karamar hukumar Toungo.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa zaben gwamnan da aka gudanar a satin da ya gabata bai kammalu ba sakamakon yawan kuri'un da aka soke sun fi tazarar dake tsakanin manyan jam'iyyun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel