Samun danyen mai ne babban bala'in da ya afkawa Najeriya - inji Sarkin Ife

Samun danyen mai ne babban bala'in da ya afkawa Najeriya - inji Sarkin Ife

Sarkin garin Ife mai daraja ta daya a yankin kasar yarbawa mai suna Oba Enitan Ogunwusi ya bayyana samuwar danyen mai a Najeriya a a matsayin babban bala'in da ya samu kasar tun da aka kirkire ta a maimakon ya zama alheri kamar sauran kasashe.

Sarkin, Oba Enitan Ogunwusi ya bayyana hakan ne a ranar Juma'ar da ta gabata yayin da yake karbar bakuncin wasu jami'an gwamnatin tarayya dake kura da harkokin shakatawar kasar watau National Executive of Nigeria Tour Operators (NATOP) a fadar sa.

Samun danyen mai ne babban bala'in da ya afkawa Najeriya - inji Sarkin Ife
Samun danyen mai ne babban bala'in da ya afkawa Najeriya - inji Sarkin Ife
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Za'a siyar da kadarorin gwamnati a zuba kudin a kasafin 2019

Su dai jami'an gwamnatin sun kai wa sarkin ziyarar ban girma ne a fadar tare da rakiyar wasu 'yan jarida inda suka bukaci masarautun gargajiya su sa bakin wajen karkato da hankalin gwamnatin tarayya akan harkokin shakatawa da yawon bude ido a kasar.

Da yake nasa jawabin, Sarkin ya yabawa tawagar tare da jinjina masu kan aikin da suke sannan kuma ya sha alwashin shigar masu gaba wajen kai bukatar su ga mahukunta a gwamnatin tarayyar.

Sarkin ya kara da cewa samuwar mai ne a Najeriya ya jefa kasar cikin halin da take ciki sakamakon fatali da dukkan sauran fannonin cigaban kasar da gwamnatocin baya suka yi wanda hakan ba karamar illa yayiwa kasar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel