INEC ta sauya ra'ayi kan zaben Bauchi, za ta sanar da sakamakon Tafawa Balewa

INEC ta sauya ra'ayi kan zaben Bauchi, za ta sanar da sakamakon Tafawa Balewa

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta amince da dawowa da ci gaban tattara sakamakon zabe a jihar Bauchi

- Za a dawo ci gaba da tattara sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa a ranar Talata 19 ga watan Maris

- INEC ta ce kwamitin binciken da ta kafa ya bada rahoton cewa har yanzu takardun sakamakon zaben rumfuna, akwatuna da kuma gundumomi na karamar hukumar

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta amince da dawowa da ci gaban tattara sakamakon zabe a jihar Bauchi.

Hukumar ta ce tattara sakamakon da sanarwar zaben karamar hukumar Tafawa Balewa a matakin kujerar gwamna zai kammala ne sakamakon cewa akwai takardun sakamakon mazabu na ainihi da ma na fotokwafi a hannun hukumar.

Za a dawo ci gaba da tattara sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa a ranar Talata 19 ga watan Maris.

KARANTA WANNAN: Kar ku kuskura ku murde zaben jihar Bauchi - PDP ta gargadi INEC

INEC ta sauya ra'ayi kan zaben Bauchi, za ta sanar da sakamakon Tafawa Balewa
INEC ta sauya ra'ayi kan zaben Bauchi, za ta sanar da sakamakon Tafawa Balewa
Asali: UGC

Hukumar ta sanar da haka a cikin wata sanarwa da ta fitar a darem ranar Juma'a daga hannun, Festus Okoye, kakakin hukumar.

Daga karshe, INEC ta dauki wadannan matakai:

  • Cewar za a ci gaba da kammala tattara sakamakon zaben.
  • Cewar za a dawo da ci gaban tattarawa tare da sanar da sakamakon zaben mazabar Tafawa Balewa a jihar Bauchi
  • Cewar kwamitin binciken da hukumar ta kafa ya bada rahoton cewa har yanzu takardun sakamakon zaben rumfuna, akwatuna da kuma gundumomi na karamar hukumar na nan a hannu.

A cewar sanarwar, hukumar ta dauki wannan matakin a wani zama na musamman da ta gudanar a ranar Talata, 12 ga watan Maris.

Taron ya yi kyakkyawan nazari kan rahoton da kwamishinan zabe na jihar Bauchi ya hada kuma ya aika mata kan yadda aka tayar da hargitsi a yayin tattara sakamakon karamar hukumar Tafawa Balerwa a cibiyar tattara sakamakon zaben, wanda ya ja aka dakatar da tattara sakamakon zaben gaba daya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel