An daure wata mata wata 6 saboda fada da makwafciya a jihar Kebbi

An daure wata mata wata 6 saboda fada da makwafciya a jihar Kebbi

Wata mata a jihar Kebbi an daure ta a gidan yari wata shidda ko kuma biyan tarar Naira dubu sha biyar saboda sabanin da ta samu da makwafciyar ta har ya kai ga sun cakusa fada a tsakanin su a kwanan baya.

Mun samu labarin hakan ne dai lokacin da uwar gidan gwamnan jihar Kebbi, Dakta Zainab ta ziyarci gidan yarin garin Birnin Kebbi, babban birnin jihar ta Kebbi inda ta ga matar da jaririn ta kafin daga bisani ta biya mata kudin tarar.

An daure wata mata wata 6 saboda fada da makwafciya a jihar Kebbi
An daure wata mata wata 6 saboda fada da makwafciya a jihar Kebbi
Asali: UGC

KU KARANTA: Sheikh Gumi ya yi tsokaci kan zaben da za'a sake Kano, Sokoto, Bauchi

Dakta Zainab ta ce akwai shire-shiren ta da ta bullu da su na biya wa fursunoni kudaden tarar da aka sa masu tare wanda take yi tare da hadin gwiwar Kungiyar Mata Lauyoyi ta Najeriya da wasu kungiyoyin.

Ta kara da cewa kungiyar su kan ziyarci gidajen yari don biyan tarar kuma a irin wannan ziyarar ne a daya daga cikin gidajen yarin da ke jihar Kebbi ta ga wannan mata.

Ta ce ta ga mata uku a daure kuma wannan matar ta fi daukar hankalinta saboda tana rike da 'yar jaririyarta.

Dakta Zainab ta ce talauci na daya daga cikin abubuwan da ke haddasa tashin hankali a wasu yankunan karkara a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel