Rikicin zabe a Taraba: Mutane 8 sun hallaka, 56 sun jikkata

Rikicin zabe a Taraba: Mutane 8 sun hallaka, 56 sun jikkata

Babbar asibitin tarayya dake Jalingo, ta tabbatar da mutuwan mutane takwas da kuma jikkatan mutane 56 wadanda ke jinya a asibitin yanzu sakamakon raunuka da suka samu a rikicin zaben da ya faru a jihar Taraba a farkon mako.

An sanya dokar ta baci a babbar birnin jihar Jalingo tun ranar Talata da aka sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar, wanda ya sabbaba rikici tsakanin yan jam'iyyun hamayya inda suka kashe juna kuma suka lalata dukiyoyin juna.

Game da adadin da asibitin ta saki, mutane biyar sun mutu kafin isowa asibiti yayinda sauran uku suka cika a cikin asibitin. Hamsin da shida na jinya; 42 a cikin suka rage a asibiti yanzu yayind aaka sallamai 12 da suka samu sauki.

Talatin da shida daga cikinsu na cikin halin mutuwa yau ko gobe, arba'in da bakwai ana kyautata zaton zasu samu sauki ba da dadewa ba, 23 sun sha sukan wuka; 6 sun jikkata sakamakon harbin bindiga, yayinda uku daga illar kwari da baka.

KU KARANTA: Muhimman abubuwan da ya kkau sani game da sabon gwamnan jihar Zamfara Mukhtar Koguna

Amma a yanzu, an rage dokar hana fitan zuwa karfe 6 zuwa 4. Amma duk da hakan, mazauna Jalingo suna tsoron fita kasuwanni da wajajen ayyukansu.

Yawancin shagunan da garin na kulle har yanzu, bankuna da kasuwanni na bude amma jama'a sun kaurace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel