Zaben Bauchi: Jami’ar tattara sakamakon Tafawa Balewa tace ana yi mata barazanar kisa

Zaben Bauchi: Jami’ar tattara sakamakon Tafawa Balewa tace ana yi mata barazanar kisa

Jami’ ar tattara sakamakon zaben gwamna na karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar Bauchi, Dominion Anosike ta bayyana cewa rayuwarta na a cikin hatsari, saboda ana yi mata barazanar kisa.

Tayi wannan ikirari ne a cikin wata wasika da ta aikawa hukumar zabe sannan ta roki hukumar da ta bayyana a gaban kwamitin bincike domin ta bayyana gaskiyar abunda ya faru har aka soke sakamakon zaben karamar hukumar.

A cikin wasikar, wadda ta aika wa Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, a ranar 13 ga watan Maris, 2019, ta amince ta bayyana ta fadi abin da ta sani, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Sai dai kuma ta yi rokon cewa ta fi so a yi zaman kwamitin a babbar birnin tarayya, Abuja, ba a Bauchi ba.

Zaben Bauchi: Jami’ar tattara sakamakon Tafawa Balewa tace ana yi mata barazanar kisa
Zaben Bauchi: Jami’ar tattara sakamakon Tafawa Balewa tace ana yi mata barazanar kisa
Asali: Instagram

Anosike ta ce ta na fuskantar barazana cewa za a kashe ta matsawar aka gan ta ko a cikin Bauchi ko a kewayen Bauchi.

“Ni ce na shugabanci zaben da aka gudanar a Karamar Hukumar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi, don haka nay i amanna cewa akwai bukatar na zo na bayar da bayanin abin da ya faru har Kwamishinan Zabe na Bauchi ya soke zaben Tafawa Balewa.” Inji Anosike.

Premium Times ta rahoto yadda jami’ar tattara sakamakon zabe na Karamar Hukumar Tafawa Balewa, Dominion Anosike ta ce ‘yan bangar siyasa sun kwace sahihin kwafen sakamakon zaben, wato Form EC 8C 1.

Babban Jami’in INEC mai bayyana sakamakon zabe, Mohammed Kyari ne ya ki amincewa da sakamakon zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa, Bayan da aka yi zargin ‘yan bangar siyasa sun hargitsa dakin taron da ake tattara sakamakon zaben.

KU KARANTA KUMA: Ku gaggauta gyaran fasalin zabe da wuri – Shugaban INEC ga majalisar dattawa

Anosike ta ce akwai sakamakon zabe na wata mazaba guda daya da aka keta kwafin takardar da ya ke ciki, sai ta yi amfani da kwamfuta ta rubuta sakamakon.

Sai dai kuma shi Kyari, ya ce ba zai yi amfani da sakamakon wanda ta rubuta ba, domin kafin ta zartas da hukunci ba ta tuntube shi ba. kuma ya ce ba ta nemi izni ko shawarar Kwamishinan Zabe na Jihar Bauchi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel