Hannun agogo: An wajabtawa matasa 9 maimata bautar kasar shekara 1 a Kano

Hannun agogo: An wajabtawa matasa 9 maimata bautar kasar shekara 1 a Kano

Shugaban hukumar bautan kasa NYSC na jihar Kano, Alhaji Ladan Baba yace matasan hukumar tara zasu maimaita shirin bautar kasar na tsawon shekara daya.

Ladan baba ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da manema labarai kan yaye matasa masu bautan kasa 2,682 da suka kammala bautarsu a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, 2019 a jihar Kano.

Game da cewarsa, matasan sun kauracewa bautar kasar daga inda aka turasu aiki na tsawon akalla watanni uku.

Baba ya kara da cewa: "Wadannan yan bautar kasar wajibi ne su maimaita shekara daya kan laifin guduwa daga wajajen aikinsu. Baya ga haka, imma ba za'a biyasu na tsawon shekaran da zasu maimaita ba, ko a biyasu rabin albashi."

Ya kara da cewa an daga wa'adin wasu matasa 21 da wata uku kuma ba za'a biyasu ba domin ladabtar dasu.

Ya laburta cewa matasa masu bautar kasa biyu sun rasa rayukansu cikin shekara dayan da ya gabata.

KU KARANTA: hadimin Ganduje ya yi murabus saboda Abba Gida-Gida

A bangare guda, Babbar asibitin tarayya dake Jalingo, ta tabbatar da mutuwan mutane takwas da kuma jikkatan mutane 56 wadanda ke jinya a asibitin yanzu sakamakon raunuka da suka samu a rikicin zaben da ya faru a jihar Taraba a farkon mako.

An sanya dokar ta baci a babbar birnin jihar Jalingo tun ranar Talata da aka sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar, wanda ya sabbaba rikici tsakanin yan jam'iyyun hamayya inda suka kashe juna kuma suka lalata dukiyoyin juna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel