Zaben 2019: Sanatocin APC da na PDP sun yi musayar yawu akan gudanarwar zabe

Zaben 2019: Sanatocin APC da na PDP sun yi musayar yawu akan gudanarwar zabe

Sanatoci daga jam’iyyar Progressives Congress (APC) da na Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Laraba, 13 ga watan Maris sun yi musayar kalamai a zauren majalisar dokokin kasar.

Sunyi musayar kalaman ne sakamakon yadda aka gudanar da zaben 2019 wanda aka kamala kwanan nan.

Sabanin ya fara ne bayan wani korafi da Sanata Dino Melaye ya gabatar wanda yayi kira ga majalisar dattawa da ta yi muhawara kan yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta gudanar da zabe a fadin kasar.

A cewarsa muhawarar zai ba da damar da majalisar dattawa za ta shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari yadda ya kamata, sannan kuma ta bukaci da ya sanya hannu a dokar zabe domin inganta zabuka anan gaba.

Zaben 2019: Sanatocin APC da na PDP sunyi musayar yawu akan gudanarwar zabe
Zaben 2019: Sanatocin APC da na PDP sunyi musayar yawu akan gudanarwar zabe
Asali: Twitter

Sai dai akan bai zamo da dadi bag a wasu sanatoci musamman na jam’iyyar APC.

Daga nan sai Shugaban masu rinjaye a majalisa, Ahmed Lawan ya mike domin tunatar da Saraki cewa hukuncinsa kan ko a bari a tattauana lamarin ko kada a tattauna ya sanya su cikin duhu.

Saraki ya jadadda cewa abun ake bukata kafin a amince da bukatar tattauna lamarin shine kaso daya cikin biyar na majalisar. Yaace kuma an samu kaso daya cikin biyar na masu barin majalisar.

KU KARANTA KUMA: Wani dan kashenin Buhari ya fara tattaki daga Abuja zuwa Kebbi

A nashi bangaren, Sanata Jibrin Barau (Kano, APC) yayi kira ga rabe majalisar domin tsayar da matsayar sanatoci kan bukatar, amma sai Saraki yayi watsi da shawarar nana, inda yace lallai abunda ake bukata shine kaso daya cikin biyar na majalisar.

Saraki ya sake bayar da tabbacin cewa sai shugabannin majalisar sun fara tantance bukatar kafin a gabatar domin yin muhawara a majalisar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel