Karar kwana: Mai juna biyu, mai makaranta, dalibai 12 suka mutu a rubzawar ginin makaranta

Karar kwana: Mai juna biyu, mai makaranta, dalibai 12 suka mutu a rubzawar ginin makaranta

Wata mata mai juna biyu, shugabar makaranta, wasu mutane 19 wanda ya hada da daliban rauda da firamare 12 sun rasa rayukansu a rubzawar gini a titin Massey, Itafaji a tsibirin Legas ranar Laraba, 13 ga watan Maris, 2019, idanuwan shaida da asibiti sun bayyana.

Amma hukumar kawo agaji na gaggawa ta kasa wato NEMA ta ce mutane takwas suka mutu kuma an ceto wasu 34 misalin karfe 10 na safe.

Hukumar kawo agaji ta jihar Legas, LASEMA bata bada wani takamammen adadin wadanda suka mutu ba amma ta ce jami'anta sun ceto mutane 10 daga cikin ginin.

Karar kwana: Mai juna biyu, mai makaranta, dalibai 12 suka mutu a rubzawar ginin makaranta
Karar kwana: Mai juna biyu, mai makaranta, dalibai 12 suka mutu a rubzawar ginin makaranta
Asali: Facebook

KU KARANTA: Babbar mota ta murkushe mutane 7 har lahira

NAN ta tattaro cea yawancin wadanda annobar ta aukawa sun mutu ne a asibiti yayinda likitoci suka gaza ceton rayuwarsu. Wannan shine abinda ya faru da wata mace mai juna biyu wacce aka ceto daga cikin amma ta mutu a asibiti.

Sauran mutane an bada rahoton cikawansu ne misalin karfe 8 na dare wanda ya hada da mai makarantar Ohen Nursery and Primary School da kuma dalibai 12.

Gidan mai tsauni hawa uku na da dakuna da yawa inda makarantar ke amfani da tsauni biyu na sama kuma wasu magidanta da iyalansu na zaune a tsauni biyu na kasa.

Ashe tun shekarar 2017 hukumar gine-ginen gwamnatin jihar Legas ta matsa lamba kan rusa ginin kasancewar ya tsufa amma mazaunan ginin suka kiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng