Shugaba Buhari ya kwace rijiyar man fetur mai lamba 11 daga hannun kamfanin Shell

Shugaba Buhari ya kwace rijiyar man fetur mai lamba 11 daga hannun kamfanin Shell

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ba rukunin kamfanonin albarkatun mai na Najeriya watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) umurnin kwace lasisin rijiyar mai mai lamba Oil Mining Lease 11 (OML 11) daga hannun kamfanin Shell.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata takardar umurni daga fadar shugaban kasar zuwa ga kamfanin na NNPC mai dauke da kwanan wata 1 ga watan Maris, da kuma lambar ofis ta SH/COS/24/A/8540 dauke da sa hannun shugaban ma'aikata, Abba Kyari.

Shugaba Buhari ya kwace rijiyar man fetur mai lamba 11 daga hannun kamfanin Shell
Shugaba Buhari ya kwace rijiyar man fetur mai lamba 11 daga hannun kamfanin Shell
Asali: UGC

A cikin takardar, shugaba Buhari ya ce NNPC din ta karbe lasisin gudanawar rijiyar kafin 30 ga watan Afrilun wannan shekarar.

Rijiyar mai ta OML 11 dai tana a yankin Neja Delta ne kuma tana da wuraren hakar danyen mai akalla 33 da ake tasta tun kusa shekarar 2017. Masana kuma sun ce kusan rijiyar ce tafi kowace muhimmanci a tarayyar Najeriya.

A wani labarin kuma, Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake da alhakin kula da albarkatun mai fetur watau Depertment for Petroleum Resources (DPR) ta sanar da cewar, an amince mata da samar da jimlar karin rijiyoyin mai guda 37 a sassa daban daban na Najeriya.

Wannan matakin da gwamnatin shugaba Buhari ta dauka dai kamar yadda muka samu daga majiyoyin an dauke shi ne domin kasar Najeriya kara yawan danyen man fetur din da ake sarrafawa ya zuwa akalla ganguna 189,850 a kullum.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel