Siyasar Zamfara: Maganar rikicin jam'iyyar APC a Zamfara ta sake tasowa

Siyasar Zamfara: Maganar rikicin jam'iyyar APC a Zamfara ta sake tasowa

Kotun daukaka kara mai zaman ta a jihar Sokoto da ta sake dage sauraren shari'ar dake gaban ta na rikicin jam'iyyar APC a jihar Zamfara bayan da bangaren da ya shigar da karar ya ce bai yadda da alkalan kotun ba sam-sam.

Kamar dai yadda muka samu, bangaren Sanata Marafa ne ya daukaka kara a Sokoto domin kalubalantar hukuncin da kotun tarayya a Gusau ta zartar cewa an yi zaben fitar da 'yan takara na jam'iyyar APC a Zamfara.

Siyasar Zamfara: Maganar rikicin jam'iyyar APC a Zamfara ta sake tasowa
Siyasar Zamfara: Maganar rikicin jam'iyyar APC a Zamfara ta sake tasowa
Asali: UGC

KU KARANTA: Sarkin Kano ya jinjinawa Kwamishinan 'yan sanda Wakili

Karar da aka dage dai na zuwa ne bayan kammala zaben gwamna a Zamfara inda hukumar zabe ta sanar da Muktar Shehu Idris dan takarar bangaren gwamnati a jam'iyyar APC da ake kalubalanta a matsayin wanda ya lashe zaben.

A baya dai kamar yadda muka samu, wata kotun daukaka kara ce dake a Abuja ta bai wa INEC umurnin ta amince da 'yan takarar APC a Zamfara, bayan da a farko INEC ta ki amincewa da 'yan takarar jam'iyyar saboda ta gaza yin zaben fitar da 'yan takara.

Rikicin na APC a Zamfara ya samo asali ne bayan da Gwamna Abdulaziz Yari ya sanar da goyon bayansa ga kwamishinansa na kudi, Alhaji Muktar Shehu Idris, a matsayin wanda zai gaje shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel