Gwamna Ganduje ya ba da tallafin firinji ga masu sana’ar kifi a kauyen Yaryasa

Gwamna Ganduje ya ba da tallafin firinji ga masu sana’ar kifi a kauyen Yaryasa

- Gwamna Abudllahi Ganduje na jihar Kano ba da gudumuwar sababbin firinji 10 ga masu sana’ar kifi a kauyen Yaryasa da ke karamar hukumar Tudun Wada

- Ganduje ya kuma ba masu sana'ar kifin su 50 tallafi dubu goma-goma

- Gwamnatin ta jihar Kano ta ce tayi wannan shiri nee domin ba yan kasuwar tallafi ta yadda za su rage asara ta hanyar daskarar da kifayensu har zuwa lokacin da za su siyar

Gwamnatin jihar Kano ta ba da gudumuwar sababbin firinji 10 ga masu sana’ar kifi a kauyen Yaryasa da ke karamar hukumar Tudun Wada don bunkasa kasuwancin su.

Jawabi wanda ya samu sa hannun Aminu Yassar, Babban darekta a harkokin sadarwa a gidan Gwamnatin Kano, yace gwamnati ta kara da gine ginen wurin turke kifaye guda hudu ga masu sana’ar kifin.

Gwamna Ganduje ya ba da tallafin firinji ga masu sana’ar kifi a kauyen Yaryasa
Gwamna Ganduje ya ba da tallafin firinji ga masu sana’ar kifi a kauyen Yaryasa
Asali: Depositphotos

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya mika firinjin tare da kudi N10,000 ga masu sana’ar kifi 50.

“Manufar yin haka ba komai bane illa taimaka muku wajen kiyaye kifaye har na tsawon kwanaki da dama ba tare da asara ba. Wannan zai inganta sana’arku ta hanyar kiyaye asara.

“Kifi na da muhimmanci cikin kayan abinci saboda haka yana da amfani sosai idan aka kiyaye su har zuwa lokacin siyar da su.”

KU KARANTA KUMA: Duk da taron dangi sai da Kwankwaso ya kai Gwamnatin Ganduje kasa – Sule Garo

Gwamnan yace, “Saboda haka, min yanke shawaran samar muku da wadannan firijin da kuma gina muku turken kidi a kasuwan don bunkasa sana’arku fiye da tsammanin ku.”

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel