Muhimman abubuwan da ya kkau sani game da sabon gwamnan jihar Zamfara Mukhtar Koguna

Muhimman abubuwan da ya kkau sani game da sabon gwamnan jihar Zamfara Mukhtar Koguna

Yayin da ake cigaba da murnar kammala zabukan gwamnoni da na 'yan majalisar jahohi a sassa daban-daban na kasar, yanzu hankula sun soma komawa akan wadanda suka samu nasarar darewa musamman ma a kujerun gwamnoni.

Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jahohin da jam'iyyar APC ta samu nasarar sake kafa gwamnati a jihar a bugu daya ba tare da zuwa zagaye na biyu ba a zaben inda Kwamishinan kudi na jihar, Alhaji Mukhtar Shehu Idris (Kogunan Gusau) ya zama gwamnan jihar.

Muhimman abubuwan da ya kkau sani game da sabon gwamnan jihar Zamfara Mukhtar Koguna
Muhimman abubuwan da ya kkau sani game da sabon gwamnan jihar Zamfara Mukhtar Koguna
Asali: Facebook

KU KARANTA: Hotunan wasu gwamnonin da suka samu nasara

Ga dai wasu daga cikin muhimman batutuwan da ya kamata ku sani game da sabon gwamnan:

1. Alh Muktan Shehu ldris cikakken dan boko ne da ke da kwarewa sosai a fannoni da dama na ilimi musamman ma kan harkokin kudi da harkokin diflomasiyya da harkokin kasa-da-kasa.

Kogunan Gusau yana da digiri na biyu a fannoni da dama daga jami'ar Bayero dake jihar Kano.

2. Alhaji Mukhtar Shehu kwararre ne a fannonin da ya karanta kuma yana da shaidar zama mamba na hukumomi da dama ciki hadda Nigerian Institute of Management (NIM) da kuma Institute of Chartered Accountant (ICAN).

3. Ta fannin kwarewa a ayyukan da yayi a baya, sabon gwamnan yayi aiki a kamfuna da dama kuma a garuruwa da dama da suka hada da Abuja da Kano kafin shigar sa siyasa.

Kamfunan da yayi aiki a baya dai sun hada da NORTHCO Holding, Abuja, Family Support Trust Fund, Chartered Bank of Nigeria, NORTHCO Holding, Abuja, intercellular NIG.LTD, Abuja da dai sauran su.

4. Ta bangaren rayuwar sa ta siyasa kuwa, Kogunan Gusau ya shiga siyasa ne a shekarar 2001 da jam'iyyar PDP kafin daga bisani ya koma jam'iyyar ANPP.

Sai dai kuma duk da cewa Gwamnan na Zamfara sau biyu yana yin takarar dan majalisar tarayya bai taba samun nasaraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel