Satar waya da dan kamfai: An yanke wa matashi hukuncin daurin shekara 6 a kurkuku

Satar waya da dan kamfai: An yanke wa matashi hukuncin daurin shekara 6 a kurkuku

- Kotu ta yanke wa wani matashi daurin shekaru shida a gidan yari

- An kama matashin ne da laifin satar wayar N6,000 da dan kamfai na mata

- Matashin ya shiga dakin wata mata ne inda ya shige bandakinta sannan ya kwace yan kamfan guda uku

Kotu ta yanke wa wani matashi dan shekaru 19 mai suna Olasunkanmi Yekini hukuncin dauri har na tsawon shekaru shida a kurkuku akan laifin satar wayar N6,000.

An kuma kama shi da laifin satar dan kamfai na mata guda uku wanda yayi sanadiyar rufe shi.

Dan sanda mai gabatar da kara, Jefani Musilimi ya fada wa kotu cewa Olasunkanmi ya aikata laifin a ranar 28 ga watan Janairu a Ibokun road, yankin Oja-Oba, Osogbo.

Satar waya da dan kamfai: An yanke wa matashi hukuncin daurin shekara 6 a kurkuku
Satar waya da dan kamfai: An yanke wa matashi hukuncin daurin shekara 6 a kurkuku
Asali: UGC

Jefani yace Olasunkanmi ya shiga dakin wata matashiya mai suna Folashade Ganiyu inda ya sace dan kamfai uku a dakin wankanta.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: PDP zata sha mamaki a zaben da za a sake a Kano - Ganduje

An gurfanar da Olasunkanmi da laifin sata da kuma yanayi dake iya kawo rashin zaman lafiya ga al’umma.

Mai gabatar da karan yace laifin ya ci karo da wassu sashin tsari na 412 da 249(d), Cap34, Volume 11 a kundin tsarin Osun 2002.

Yayin da take yanke hukunci, mai shari’a Rofiat Olayemi tace Olusaunlanmi ya kasance mai laifi kuma an yanke mishi hukuncin shafe shekaru shida a gidan yari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel