Zaben Gombe: Nafada ya taya Yahaya murnar lashe zabe, ya ce ba zai je kotu ba

Zaben Gombe: Nafada ya taya Yahaya murnar lashe zabe, ya ce ba zai je kotu ba

A yayin da ake ci gaba da yin tsokaci kan sakamakon zaben da aka sanar na zaben gwamnan jihar Gombe da ya gudana a ranar Asabar, manyan masu ruwa da tsaki sun fara bayyana matakan da za su dauka na gaba tare da dan takarar PDP da ya sha kaye, Sanata Usman Bayero Nafada, wanda ya bayyana cewa zai shawarci jam'iyyarsa akan kauracewa sakamakon zaben da aka sanar da kuma kin zuwa kotun daukaka karar zaben.

Bayero Nafada a yayin zantawarsa da manema labarai a karon farko, awanni 24 bayan sanar da sakamakon zaben, ya ce jam'iyyarsu ta fuskanci wulakanci da tsangwama daga jami'an tsaro a yayin zaben, wanda har ta kai ga cafke wasu manyan jam'iyyar bayan kammala zaben ba tare da dalili ba. Sai dai, ya bayyana sakamakon zaben a matsayin kaddara ta ubangiji.

Bayero Nafada, wanda a yanzu haka yake kujerar majalisar dattijai, ya taya wanda ya lashe zaben murna, amma ya ce bin kadin sakamakon zaben na wuyan jam'iyyar sai dai zai shawarceta da kauracewa hakan saboda a cewarsa, ba shi da ra'ayin zuwa kotu kuma bai san matakin da ita jam'iyyar ta dauka fa.

KARANTA WANNAN: Zaben gwamnoni: Maku ya ki amincewa da sakamakon zaben jihar Nasarawa

Zaben Gombe: Nafada ya taya Yahaya murnar lashe zabe, ya ce ba zai je kotu ba
Zaben Gombe: Nafada ya taya Yahaya murnar lashe zabe, ya ce ba zai je kotu ba
Asali: UGC

Sai dai, a yayin taya wanda ya lashe zaben gwamnan jihar murna, Mohammed Inuwwa Yahaya na jam'iyyar APC, Bayero Nafada ya ce, "bari na yi amfani da wannan damar wajen taya shi murna, amma taya shi murna ba wai yana nufin jam'iyya ba za ta dau mataki ba. Amma ni dai ba ni da wata matsala da shi."

Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da dukkanin wadanda suka kada masa kuri'a da suka kasance cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yana mai cewa, "Wannan zai taimaka gaya, sau tari muna ganin irin hakan, kawai lokaci ne na shekaru hudu, koma menene, zamu sake dawowa fagen fama, ma damar muna raye, zamu dawo, domin hakan, ina ganin babu wata matsala."

Da ya ke jawabin godiya kan wannan nasara da ya samu, Mohammed Inuwa Yahaya wanda ya godewa Allah da ganin cewa an gudanar da sahihin zabe mai cike da kwanciyar hankali, ya ce a yanzu al'ummar jihar Gombe sai su zauna zaman jiran gwamnatin da tai daban da ta baya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel