Zaben gwamnoni: Maku ya ki amincewa da sakamakon zaben jihar Nasarawa

Zaben gwamnoni: Maku ya ki amincewa da sakamakon zaben jihar Nasarawa

- Hon. Labaran Maku, dan takarar gwamnan jihar Nasarawa karkashin jam'iyyar APGA ya ki amincewa da sakamakon zaben gwamnan jihar

- A cewarsa, an tafka magudi da kuma kura-kurai wanda hukuamr INEC tare da hadin guiwar jami'an tsaro suka yi hadaka wajen yi

- Dan takarar ya kuma yi ikirarin cewa an yi watsi da ka'idojin zabe a garuruwan Toto, Wamba, wasu sassa na Lafia, Awe da Keffi

Hon. Labaran Maku, dan takarar gwamnan jihar Nasarawa karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ya ki amincewa da sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar 9 ga watan Maris akan abunda ya kira "damfara da magudi".

Ya bayyana hakan a kauyen Wakama da ke Nasarawa Eggon a yayin da ya ke tsokaci kan sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar na jihar a ranar Litinin.

A cewarsa, an tafka magudi da kuma kura-kurai wanda hukuamr INEC tare da hadin guiwar jami'an tsaro suka yi hadaka wajen yi.

KARANTA WANNAN: Zaben 2019: INEC ba ta tabuka komai ba, dole Yakubu ya yi murabus - Onitiri

Zaben gwamnoni: Maku ya ki amincewa da sakamakon zaben jihar Nasarawa
Zaben gwamnoni: Maku ya ki amincewa da sakamakon zaben jihar Nasarawa
Asali: UGC

Maku ya ce jam'iyyarsu ta APGA ta ki amincewa da sakamakon zaben ne saboda ganin cewa sakamakon zaben bai haska gaskiyar kuri'un da jama'ar jihar suka kada ba, akan hakan ya zama tilas garesu su yi Allah wadai da zaben.

"Gwamnatin jam'iyyar APC ta hada kai da INEC da jami'an tsaro wajen sanar da sakamakon zabe tun kafin ma a kammala tattara sakamakon zaben.

"Sun yanke hukuncin sanya APGA a matsayin wacce ta zo na ukku da nufin rufe mana baki wajen shelar cewa jama'a na tare da mu," a cewar Maku.

Dan takarar ya kuma yi ikirarin cewa an yi watsi da ka'idojin zabe a garuruwan Toto, Wamba, wasu sassa na Lafia, Awe da Keffi.

"Ba a yi amfani da na'urar tantance masu kad'a kuri'a ba a wasu yankuna saboda cimma manufarsu. Sun kawo sakamakon zaben Toto da wasu garurwa da rikicin zabe ya shafa," a cewar Maku.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel