PDP ta zama mafi rinjaye a majalisar dokokin Abia bayan lashe kujeru 19 cikin 24

PDP ta zama mafi rinjaye a majalisar dokokin Abia bayan lashe kujeru 19 cikin 24

- Jam'iyyar PDP a jihar Abia ta samu nasarar lashe kujeru 19 cikin 24 na majalisar dokokin jihar

- Yan takara 385 ne suka tsaya takara karkashin jam'iyyu 43 inda jam'iyyar APGA ta lashe kujeru ukkuj, yayin da jam'iyyar APC ta lashe kujeru biyu

- 12 daga cikin wadanda suka lashe zaben za su koma ne a karo na biyu, yayin da sauran 'yan takarar 12 za su je majalisar ne a karon farko

Jam'iyyar PDP a jihar Abia ta samu nasarar lashe kujeru 19 cikin 24 na majalisar dokokin jihar, bayan kammala zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki da aka gudanar a ranar Asabar 9 ga watan Maris.

Mr Joseph Iloh, jami'in tattara sakamakon zabe na hukumar INEC a jihar, ya bayyana sakamakon zaben ranar 9 ga watan Maris ga manema labarai a Umuahia.

Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa 'yan takara 385 ne suka tsaya takara karkashin jam'iyyu 43 domin takarar kujerun majalisar dokokin jihar guda 24, inda jam'iyyar APGA ta lashe kujeru ukku, yayin da jam'iyyar APC ta lashe kujeru biyu.

KARANTA WANNAN: Jihohin Bauchi, Kano, Sokoto, Rivers da sauransu za su san makomarsu yau - INEC

PDP ta zama mafi rinjaye a majalisar dokokin Abia bayan lashe kujeru 19 cikin 24
PDP ta zama mafi rinjaye a majalisar dokokin Abia bayan lashe kujeru 19 cikin 24
Asali: Twitter

Bayani dalla dalla kan sakamakon zaben ya nuna cewa PDP ta lashe kujerun mazabar Aba ta Arewa, Bende ta Kudu, Ikwuano, Isiala Ngwa ta Arewa da kuma Isiala Ngwa. Sauran mazabun sun hada da Obingwa ta Gabas, Obingwa ta Yamma, Ohafia ta Arewa, Ohafia ta Kudu, Osisioma ta Arewa da kuma Osisioma ta Kudu.

Daga cikin kujerun da PDP ta lashe har ila yau sun hada da Ugwunagbo, Ukwa ta Gabas, Ukwa ta Yamma, Umuahia ta Arewa, Umuahia ta Tsakiya, Umunneochi, Umuahia ta Gabas da kuma Umuahia ta Kudu.

Jam'iyyar APGA kuwa ta lashe kujerun mazabar Arochukwu, Aba ta Arewa da Aba a Kudu, yayin da APC ta lashe kujerun mazabar Bende ta Kudu da Isuikwato.

NAN ta ruwaito cewa 12 daga cikin wadanda suka lashe zaben za su koma ne a karo na biyu, yayin da sauran 'yan takarar 12 da suka lashe zaben za su je majalisar ne a karon farko.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel