An nemi sunan wani gwamnan APC an rasa a jerin sunayen Sanatocin da suka samu nasara

An nemi sunan wani gwamnan APC an rasa a jerin sunayen Sanatocin da suka samu nasara

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) ta cire sunan gwamnan jihar Imo, dan jam'iyyar APC mai suna Rochas Okorocha daga jerin sunayen Sanatocin da suka samu nasara a zaben da ya gudana.

Kamar yadda muka samu, hukumar zaben ta Independent National Electoral Commission (INEC) ta saka sunayen wadanda suka samu nasa a zabukan shugaban kasa da kuma na 'yan majalisar tarayya a shafin ta na yanar gizo da ta ce za ta baiwa satifiket.

An nemi sunan wani gwamnan APC an rasa a jerin sunayen Sanatocin da suka samu nasara
An nemi sunan wani gwamnan APC an rasa a jerin sunayen Sanatocin da suka samu nasara
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Arewa na bukatar jagora irin Kwankwaso

Sai dai kamar yadda muka lura, a jihar ta Imo, sunan Sanata Onyewuchi Ezenwa Francis da ya lashe zabe a PDP ne kadan a jerin sunayen sanatocin da INEC ta ce za ta baiwa Satifiket.

A wurin da ya kamata a saka sunan Gwamna Okorocha, hukumar ta INEC sai ta rubuta cewa 'Nasarar da aka bayyana a baya cikin matsi jami'an su suka yi ta'.

A wani labarin kuma, Jami'an tsaro sun cafke wani jami’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC dake da alhakin tattara sakamakon zabe a karamar hukumar Ohaji Egbema ta jihar Imo mai suna Kelechi Ezirim saboda zargin samun sa da laifin tafka magukin zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel