Zaben 2019: Jam'iyyar APC ta lashe rumfar Shugaba Buhari da gagarumin rinjaye

Zaben 2019: Jam'iyyar APC ta lashe rumfar Shugaba Buhari da gagarumin rinjaye

Jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) a jihar Katsina ta lashe zaben gwamna da na dan majalisar jiha a rumfar shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Sakamakon zaben rumfar da muka samu na rumfar shugaban kasar watau rumfar ta 003, a mazabar Sarkin Yara A ta jihar Daura na nuni ne da cewa jam'iyyar ta APC ta lashe zaben ne da gagarumin rinjaye.

Zaben 2019: Jam'iyyar APC ta lashe rumfar Shugaba Buhari da gagarumin rinjaye
Zaben 2019: Jam'iyyar APC ta lashe rumfar Shugaba Buhari da gagarumin rinjaye
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sakamakon zaben gwamna da 'yan majalisa a Zamfara da Katsina

Legit.ng Hausa ta samu cewa Gwamnan jihar ta Katsina, Aminu Bello Masari na jam'iyyar APC samu kuri'u 370 yayin da dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP, Sanata Yakubu Lado Danmarke ya samu kuri'u 42 kacal.

Haka ma dai a zaben kujerar dan majalisar jiha jam'iyyar APC ta samu kuri'u 368 yayin da ita kuma PDP ta samu kuri'u 42.

A wani labarin kuma, Akalla mutane takwas ne suka jikkata a yayin wani artabu a tsakanin magoya bayan manyan jam'iyyun Peoples Democratic Party (PDP) da kuma All Progressives Congress (APC) a mazaba ta 9 rumfa ta 007 a karamar hukumar nsit Atai, jihar Akwa Ibom.

Sai dai bayanan kuma rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu sun bayyana mana cewa mafiya yawan wadanda suka ji raunin a sakamakon fadan 'yan jam'iyyar APC kuma tuni har an kai su wata asibi mafi kusa domin karbar kulawar likita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel