KAI TSAYE: Sakamakon zaben kujerar gwamna a jihohin Borno, Adamawa da Yobe

KAI TSAYE: Sakamakon zaben kujerar gwamna a jihohin Borno, Adamawa da Yobe

Biyo bayan zaben kujerar gwamnoni da 'yan majalisun dokoki da aka gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris, 2019, za mu ci gaba da kawo muku yadda sakamakon zaben ke kaya wa cikin jihohin Borno, Yobe da kuma Adamawa.

Tirya Tiryan ya ga yadda sakamakon zaben ke kasancewa kamar yadda Turawan Zabe da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta wakilta a jihohin Borno, Yobe da kuma Adamawa.

Jihar Borno

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta tabbatar da nasarar 'dan takarar gwamnan jihar Borno na jam'iyyar APC, Farfesa Babagana Umara Zulum wanda ya samu kuri’u 1,175,440. Farfesa Zulum ya doke babban abokin adawarsa, Muhammad Alkali Imam na jam’iyyar PDP, wanda ya samu kuri’u 66,115 kacal.

Farfesa Babagana Umar Zulum
Farfesa Babagana Umar Zulum
Asali: Getty Images

Karamar Hukumar Mafa

APC: 53,011

PDP: 163

Karamar Hukumar Ngala

APC: 42,409

PDP: 1,942

Karamar Hukumar Magumeri

APC: 22,261

PDP: 122

Jihar Yobe

Da sanadin shafin jaridar The Cable mun samu cewa, dan takarar kujerar gwamnan jihar Yobe a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, ya lashe zaben gwamnan jihar Yobe kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta zayyana.

Rahotanni sun bayyana cewa, Mai Mala Buni, ya lashe zaben gwamnan jihar Yobe da kimanin kuri'u 444,013, inda ya lallasa babban abokin adawar sa na jam'iyyar PDP, Umar Bello Iliya, da ya samu gamayyar kuri'u 95,703.

Mai Mala Buni
Mai Mala Buni
Asali: Original

A jiya Lahadi jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, dan takarar kujerar gwamnan jihar Yobe a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, shine ke kan gaba yayin da lashe sakamakon zaben kananan hukumomi 9 na jihar Yobe.

Karamar Hukumar Damaturu

APC: 26,087

PDP: 3,760

Karamar Hukumar Bade

APC: 32,213

PDP: 8,854

Karamar Hukumar Karasuwa

APC: 24,263

PDP: 2,762

Karamar Hukumar Bursari

APC: 20,657

PDP: 2,813

Karamar Hukumar Gulani

APC: 21,765

PDP: 4,576

Karamar Hukumar Fika

APC: 36,519

PDP: 9,552

Karamar Hukumar Tarmuwa

APC: 11,338

PDP: 3,925

Karamar Hukumar Nangere

APC: 25,698

PDP: 4,765

Karamar Hukumar Gujba

APC: 17,714

PDP: 1,119

Jihar Adamawa

Karamar Hukumar Mubi North

APC: 31,794

PDP: 16,667

Karamar Hukumar Yola North

APC: 20,979

PDP: 24,383

Karamar Hukumar Song

APC: 17,439

PDP: 24,764

Karamar Hukumar Michika

APC: 13,224

PDP: 24,504

Karamar Hukumar Shelleng

APC: 15,880

PDP: 11,139

Karamar Hukumar Yola South

APC: 21,941

PDP: 17,432

Karamar Hukumar Mayo-Belwa

APC: 14,198

PDP: 19,897

Karamar Hukumar Girei

APC: 14,976

PDP: 14,115

Adamawa State, Girei LGA

APC:14,976

PDP: 14,115

Adamawa

Shelleng LGA.

ADC: 3699

APC:15,880

PDP: 11,135

Mubi North LG

APC - 31,794

PDP - 16,667

ADC - 2,810

ANP - 91

SDP - 883

Borno: Ngala LGA

APC: 42,409

PDP: 1942

Borno: Magumeri LGA

APC: 22,261

PDP: 122

Dan takaran kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alh Atiku Abubakar, ya kada kuri'arrsa a garin Yola, jihar Adamawa. Yayi kira ga jama'a su kada kuri'unsu cikin lumana kuma su kare kuri'unsu.

Yace: "Na kada kuri'ata yau a rumfar zabena dake Yola. Ina kira ga dukkan wadanda basuyi zabe ba su yi cikin lumana kuma su kare zabensu."

Gwamnan jihar Adamawa, Bidow Jibrilla, ya kada kuri'arsa a Manawachi 01 PU dake Mubi, jihar Adamawa.

KAI TSAYE: Yadda zaben gwamnoni ke gudana a jihohin Borno, Adamawa da Yobe
Adamawa da Yobe
Asali: Facebook

KARANTA KUMA: Yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Kano ke kasancewa

KAI TSAYE: Yadda zaben gwamnoni ke gudana a jihohin Borno, Adamawa da Yobe
KAI TSAYE: Yadda zaben gwamnoni ke gudana a jihohin Borno, Adamawa da Yobe
Asali: Facebook

Allah ya kawo ranar zaben gwamnoni da yan majalisun dokokin jiha inda zamu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a jihohin Borno, Yobe da Adamawa kai tsaye.

Da farko, zamu kawo muku manyan yan takara a wadannan jihohi da jam'iyyunsu:

Jihar Adamawa:

1. Ahmed Fintiri PDP

2. Jibrilla Bindow APC

3. Mohammad Nyako ADC

Jihar Borno:

1. Babagana Umarar Zulum APC

2. Mohammed Imam PDP

Jihar Yobe:

1. Mai Mala Buni APC

2. Umar Iliya Damagum PDP

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel