Yanzu-yanzu- Rikici ya barke a Jalingo, an dabawa mutum daya wuka

Yanzu-yanzu- Rikici ya barke a Jalingo, an dabawa mutum daya wuka

An tura jami'an yan sanda garin Jalingo, babbar birnin jihar Taraba doin kwantar da kuran rikicin kabilancin da ta faru a Jeka da Fari, kusa da gidan gwamnatin jihar.

Tashin hankalin ya fara ne yayinda aka dabawa wani matashi wuka. Kawai sai yan uwan wanda aka raunata suka kai mumunan hari kan kabilar Hausa/Fulani dake unguwar.

Rahotanni sun nuna cewa an lalata dukiyoyin jama'a kuma an jikkata daruruwan mutane, yara da mata. An yanzu haka, da dama sun gudu daga muhallansu, wasu kuma suna boye cikin gidajensu.

KU KARANTA: Zaben gobe: Jerin yawan masu takarar gwamna jiha-jiha

Wani mazanin unguwar, Yakubu Sabo, ya bayyanawa jaridar Daily Trust cewa rikicin ya fara ne yayinda wasu matasan Mumuye suka amsa kudi a gidan gwamnatin jihar domin rabawa matasan gwamna Darius Ishaku amma suka gudu da kudin.

Yayinda matasan suka kama wanda ya gudu da kudin, sai suka daba masa wuka. Maimakon matasan Mumuye su bi wadanda suka dabawa dan uwansu wuka, sai suka kai Hausa/Fulani da babu ruwansu hari ana zaune kalau.

A yanzu haka, yan kasuwan a Jalingo sun kulle shagunansu sakamakon tsoro abinda zai biyo baya.

A bangare guda, Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da shari'ar da babban kotun tarayya da ke zauna a Legas ta zantar na kwace kudi mallakan uwargidar tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, Patience Jonathan, dala milyan takwas a dubu dari hudu.

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gano wasu makudan kudi a asusunan banki daban-daban da Patience Jonathan ta boye kudin ba ba zata iya bayanin yadda ta samesu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel