Lafiya jari: Anfanin 'ya'yan agwaluma 10 na ban mamaki a jikin dan adam

Lafiya jari: Anfanin 'ya'yan agwaluma 10 na ban mamaki a jikin dan adam

A cigaba da kawo maku labaru akan ababen marmari da kuma abinciccika masu karin lafiya da dumbin baiwa da Allah ya ajiye a cikin su, yau ma kuma gamu dauke da wani diyan iccen mai dumbin anfani na ban mamaki a tattare da shi mai suna Agwaluma.

Wani babban likita masanin abincin da ke gina jikin dan adam, Dakta Andrew Marbell, ya ce; wannan dan icen da aka fi sani da Agwaluma ya na da matukar anfani sakamakon binciken da masana suka yi sosai a kan sa.

Lafiya jari: Anfanin 'ya'yan agwaluma 10 na ban mamaki a jikin dan adam
Lafiya jari: Anfanin 'ya'yan agwaluma 10 na ban mamaki a jikin dan adam
Asali: Facebook

KU KARANTA: Buhari zai sayar da dam-dam din Najeriya 6 ga 'yan kasuwa

Likitan ya bayyana hakan ne ga manema labarai yau Alhamis a garin Abuja, a cewarshi Agwaluman ta na dauke da sinadarin “Vitamin C” kuma adadin sinadarin yafi na wanda yake cikin lemun zaki

Legit.ng Hausa dai ta tattaro maku wasu daga cikin anfanin na diyan iccen, kuma ga su kamar haka:

1. Agwaluma na taimakawa wajen rage suga a cikin jini,

2. Yana na rage kitse a jikin mutum,

3. Ya na matukar taimakawa wajen kiyaye kamowa da cutar ciwon zuciya.

4. Yana kare jikin mutum daga cutr kaikayin makoshi,

5. Agwaluma na maganin coshewar ciki

6. Haka ma yana maganin ciwon hakuri.

7. Ana amfani da ‘ya’yan agwalumar a matsayin maganin cutukkan fata.

8. Cin ‘ya’yan agwaluma na taimakawa mutum wajen hana shi kamuwa da cutar kansa.

9. Bawon bishiyar yana magance tari, da shawara.

10. Agwaluma na na karawa mata musu karfin jiki sosai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel