Sarkin Kano ya yiwa mahaifiyar Sheik Aminu Daura Sallar Jana'iza

Sarkin Kano ya yiwa mahaifiyar Sheik Aminu Daura Sallar Jana'iza

Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu a ranar Alhamis ya jagoranci Sallar Jana'izar mahaifiyar kwamandan hukumar Hizbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, a Karkasara, karamar hukumar Tarauni na jihar Kano.

Hajiya Sa'adatu Almu ta rasu a daren Laraba, 6 ga watan Maris, 2019 tana mai shekaru 84.

Jaridar Daily Nigerian ta bayyana cewa wannan shine karo na farko da sarkin zai jagoranci sallar jana'izar a wajen fada tun lokacin ya hau mulki a shekarar 2014.

Magabacinsa, Marigayi Sarki Ado Bayero, bai halarci sallar jana'iza ba illa yan kalilan, har da na shahrarren attajiri Sani Marshal da Sheik Abe a shekaru 50 da yayi akan mulki.

Mun kawo muku cewa Shahararren malamin addinin nan, kuma shugaban hukumar Hisbah ta jahar Kano, Sheikh Aminu Daurawa, ya yi rashin mahaifiyarsa, kamar yadda Shehin Malamin ya bayyana da kansa.

Legit.ng ta ruwaito Daurawa ya bayyana haka ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda yace za’a gudanar da jana’izar mahaifiyar tasa ne a gidansa dake unguwar Yar Akwa, cikin garin Kano.

KU KARANTA: Wajibi ne PDP ta yiwa yan Najeriya bayani kan arzikin da tayi watanda - Buhari

“Inna lillah wa inna ilaihi rajiun Allah ya yiwa Hajiya babata rasuwa zaayi Janaiza a gidana na Unguwar yar akwa kusa da Darussunnah ko makarantar zam zam da misalin karfe sha daya na safe inshaa Allahu” Inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel