Shugabannin Fulanin PDP 66 da mabiyansu 1000 sun koma APC gaab da zabe

Shugabannin Fulanin PDP 66 da mabiyansu 1000 sun koma APC gaab da zabe

Akalla shugabannin kungiyar Fulani 66 tare da yan arewa 1000 daga kananan hukumomin Silame, Wamakko, Tangaza, Gudu, Yabo, Shagari, Binji da Tureta duk a jihar Sokoto , sun bayyana komawar su jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Laraba, 6 ga watan Maris.

Shugaban jam’iyyar APC na kungiyar Fulani a fadin kasa, Alhaji Shehu Aliyu ya bayyana cewa masu sauya shekar sun bar tsohuwar jam’iyyar su ne saboda sakacin shuwagabannin PDP, sannan ya kara da cewa a halin yanzu alúmman Fulani na fuskantar barazanar rashin isasshen wuraren kiwon dabbobi.

Yace shuwagabannin tare da magoya bayan su sun yanke shawaran hada kai da APC, tare da gudanar da ayyuka don tabbatar da nasarar yan takaranta a lokacin zabbukan gwamnoni da yan majalisan jiha.

Shugabannin Fulanin PDP 66 da mabiyansu 1000 sun koma APC gaab da zabe
Shugabannin Fulanin PDP 66 da mabiyansu 1000 sun koma APC gaab da zabe
Asali: UGC

Yayin da yake magana, shugaban kwamitin dattijan APC, Alhaji Aminu Tambari Tafida, ya sha alwashin cewa za a biya wa Fulanawa bukatunsu idan Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto da Faruk Malami Yabo suka yi nasara a zabe, In sha Allah.

KU KARANTA KUMA: Jagoran kungiyar matasan Atiku ya sauya sheka zuwa APC, ya sha alwashin mara wa Zulum baya

Shugaban jam’iyyanr a na jihar, Alhaji Isah Sadiq Achida, yayi kira ga yan Fulani a fadin jihar da su fito kwansu da kwarkwatan su a ranar Asabar don zaban yan takarar jam’iyyar.

Alhaji Isa Sadiq Achida ya sha alwashin cewa gwamnati wacce APC ke jagoranta za ta mayar da hankali a matakai da zasu biya wa Fulani da dabbobin su bukatun su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel