Dangote ne kan gaba a tsakanin attajirai mafi arziki a cikin bakaken fata

Dangote ne kan gaba a tsakanin attajirai mafi arziki a cikin bakaken fata

Fitaccen attajirin nan dan asalin jahar Kano, Aliko Dangote ne kan gaba a jerin bakaken fata guda goma sha uku da suka fi dimbin arziki a duniya, kamar yadda binciken jaridar Forbes ta nuna a shekarar 2019.

Legit.ng ta ruwaito Dangote ya rike wannan kambu ne bayan binciken jaridar Forbes ya nuna karfin arzikinsa ya kai dala biliyan goma da miliyan dari tara, wanda ya samesu a harkar sarrafa siga, siminti da kuma fulawa.

KU KARANTA: Katafaren kamfanin sarrafa tumatir na Dangote dake jahar Kano ya fara aiki

Dangote ne kan gaba a tsakanin attajirai mafi arziki a cikin bakaken fata
Dangote-Abdulsamad
Asali: UGC

Sai dai akwai wani katafaren matatar mai mallaki Dangote wanda ya gina a jahar Legas da yanzu haka yake gab da fara aiki, inda zai dinga tace gangar mai dubu dari shida da hamsin a duk rana, fiye da abinda gaba daya matatun man Najeriya guda uku zasu iya tacewa.

Mai bi masa a jerin bakaken fata da suka fi arziki a Najeriya shine Mike Adenuga, shugaban kamfanin sadarwar na Globacom, masu layin Glo, wanda aka auna arzikinsa ya kai dala biliyan tara da miliyan dari.

Ga dai cikakken jerin attajirai bakaken fata su goma sha uku da suka fi arziki a duniya, kamar yadda jaridar Forbes ta tattara;

1. Aliko Dangote – Dan Najeriya ($10.9bn)

2. Mike Adenuga – Dan Najeriya ($9.1 bn)

3. Robert Smith – Ba’amurke ($5 bn)

4. David Steward – Ba’amurke ($3 bn)

5. Oprah Winfrey – Ba’amurkiya ($2.5 bn)

6. Strive Masiyiwa – Dan Zimbabwe ($2.4 bn)

7. Isabel Dos Santos – Yar Angola ($2.3 bn)

8. Patrice Motsepe – Dan Afirka ta kudu ($2.3 bn)

9. Michael Jordan – Ba’amurke ($1.9 bn)

10. Michael Lee-Chin – Dan Kanada ($1.9 bn)

11. Abdulsamad Rabiu – Dan Najeriya ($1.6 bn)

12. Folorunsho Alakija – Yar Najeriya ($1.1 bn)

13. Mohammed Ibrahim – Dan Sudan ($1.1 bn)

A wani laabrin kuma katafaren kamfanin sarrafa tumati da fitaccen attajirin nan Alhaji Aliko Dangote ya bude a garin Kadawa na jahar Kano ta fara aiki ganga ganga, bincike ya nuna a duk nahiyar Afirka babu wata kamfanin sarrafa tumatir da ta kai wannan girma.

Shugaban kamfanin, Malam Abdulkareem Kaita ya bayyana cewa kamfanin dake sarrafa tan dubu daya da dari biyu (1,200tons) na danyen tumatir ya fara aiki bayan kammala duk wasu shirye shirye da tsare tsare.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel