Mai-ran-karfe: Wata tsohuwa 'yar shekara 68 ta shiga furamare aji 1

Mai-ran-karfe: Wata tsohuwa 'yar shekara 68 ta shiga furamare aji 1

Lallai maganar Hausawa gaskiya ne da suka ce gemu baya hana ilimi ga dukkan wanda yake da sha'awar hakan domin kuma mun samu labarin wata tsohuwa mai shekaru 68 a duniya da ta koma makarantar Furamare a kasar Kenya.

Matar mai suna Veronicah Kaleso kmar yadda muka samu ta koma makarantar ne sannan kuma ta zana jarabawar kammala furamare tare da sauran 'yan kasar a makarantar Unoa dake a garin Makueni.

Mai-ran-karfe: Wata tsohuwa 'yar shekara 68 ta shiga furamare aji 1
Mai-ran-karfe: Wata tsohuwa 'yar shekara 68 ta shiga furamare aji 1
Asali: UGC

KU KARANTA: Ana kishin-kishin din auren Nafisa Abdullahi ya taso

Legit.ng Hausa ta samu cewa Veronicah Kaleso ta bar makaranta ne tun a shekarun 1960 amma bata samu ta koma ba sai a wannan lokacin domin ta inganta rayuwar ta da ta sauran al'umma, kamar yadda tace.

Veronicah Kaleso ta kara da cewa ta koma makaranta ne domin ta kara samun ilimin gudanar da sana'ar ta ta noma domin a halin yanzu zamani ya zo da abubuwa da dama da suke bukatar ilimin zamani.

Labarin Veronicah dai na zaman tamkar na karfafa gwuiwa ga sauran mutanen da ke ganin tsufa ko yawan shekaru sun zama tamkar katangar da zata hana su cigaba da karatu ko kuma sabuwar rayuwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel