Gaba-da-gaban-ta: Wata matashiyar 'yar kwalisa ta yi wa shugaban kamfanin Fesbuk tsiya

Gaba-da-gaban-ta: Wata matashiyar 'yar kwalisa ta yi wa shugaban kamfanin Fesbuk tsiya

Wata matashiyar 'yar kwalisa mai suna Kylie Jenner ta zamo matashiyar da ta karya tarihin da shugaban dandalin sadarwar zamani na Fesbuk ya kafa yayin da ta fi tsararrakinta tarin arziki a duniya, a cewar Mujallar Forbes a jerin sunayen masu arziki da ta fitar.

Matashiyar, 'yar zuri'ar fitattun iyalan nan na Kardashian, ta samu arzikinta sakamakon sayar da kayan kwalliya da take yi a kasar Amurka da ma sassan duniya baki daya.

Gaba-da-gaban-ta: Wata matashiyar 'yar kwalisa ta yi wa shugaban kamfanin Fesbuk tsiya
Gaba-da-gaban-ta: Wata matashiyar 'yar kwalisa ta yi wa shugaban kamfanin Fesbuk tsiya
Asali: Instagram

KU KARANTA: Najeriya ta samu babban matsayi a majalisar dinkin duniya

Matsahiyar mai shekara 21, tana da kamfanin samar da kayan kwalliya na Kylie Cosmetics, kasuwancin da ta fara shekara uku da suka gabata, wanda a shekarar da ta gabata kadai ta yi cinikin dala miliyan 360.

Ta kai wannan matsayi ne a shekarun da ba su kai na shugaban Facebook Mark Zuckerberg ba, wanda ya zama biloniya yana dan shekara 23.

Da take jawabi akan wannan sabon matsayin nata, matasiyat sai ta kada baki tace "Ban tsammaci komai ba. Ban hango hakan zai faru a gaba ba.

"Amma na ji dadin karramawar. Wannan kara min azama ne aka yi," kamar yadda Ms Jenner ta shaida wa Forbes.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel