Zaben gwamnoni: Shugaba Buhari ya bukaci magoya bayan sa suyi APC Sak

Zaben gwamnoni: Shugaba Buhari ya bukaci magoya bayan sa suyi APC Sak

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga magoya bayan sa da dukkan masu jefa kuri’a da su zabi ’yan jam’iyyar sa ta APC daga sama har kasa, domin hakan ne kadai zai taimaka ma sa wajen hanzarta cimma burinsa na Mataki na gaba, watau ‘Next Level’.

Shugaban kasar dai ya bayyana hakan ne ranar Laraba cikin wani sakonsa da ya aike ga ’yan Najeriya kan zaben da za a gudanar ranar 9 ga Maris, 2019 na gwamnoni da ’yan majalisun jihohi a dukkan fadin kasar in banda jahohi 7 kacal.

Zaben gwamnoni: Shugaba Buhari ya bukaci magoya bayan sa suyi APC Sak
Zaben gwamnoni: Shugaba Buhari ya bukaci magoya bayan sa suyi APC Sak
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Shekarau yayi fitowa ta musamman a fim din Hausa

Legit.ng Hausa ta samu cewa a cikin sakon na bidiyon mai mintuna 3:35, Buhari ya ce, “a matsayi na na dan jam’iyyar APC, ina mai gabatar da ‘yan takararmu gaba daya gare ku, domin idan ku ka zabe su, mu na da kyawawan manufofi da akidu managarta na cigaba kamar ni."

Haka ma shugaban ya kuma yi kira ga ’yan kasar da su fito kwan su da kwarkwata wajen zaben kuma cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba tare tayar da zaune tsaye ba su kada kuri’un su, ya na mai cewa, dukkan zabubbukan su na da amfani kamar yadda wadanda aka yi a baya suke da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel