Labaran waje: An samu sabani tsakanin Sarkin Saudiyya da Yarima mai jira gado MBS

Labaran waje: An samu sabani tsakanin Sarkin Saudiyya da Yarima mai jira gado MBS

Da alamun sabani ya kunno kai tsakanin mai martaba sarkin Saudiyya, Malik Salman da 'dansa kuma yarima mai jiran gado, Muhammad bin Salman kan wasu abubuwa da ya tattari rikicin kasar Yemen. Jaridar Guardia ta Ingila ta bada rahoto ranan Talata.

Rahoton ya bayyana cewa sabanin ya fara bayyana ne yayinda sarki Salman ya kai ziyara kasar Masar a watan Febrairu inda masu bashi shawara suka jawo hankalinsa kan wani tuggu da haifaffen cikinsa ke shirya masa.

Majiya da aka sakaye sunansa ya bayyana cewa na hannun daman sarkin sun damu matuka da wannan labari har ya kai aka cire dukkan dogaran sarkin kuma aka maye gurginsu da wasu amintattu 30.

Labaran waje: An samu sabani tsakanin Sarkin Saudiyya da Yarima mai jira gado MBS
Labaran waje: An samu sabani tsakanin Sarkin Saudiyya da Yarima mai jira gado MBS
Asali: UGC

Kana har wasu jami'an tsaron kasar Masar abin ya shafa inda aka sallamesu daga bakin aiki bisa ga zargin da akeyi akansu.

Yayinda sarkin ya koma gida Saudiyya, Yarima Muhammad bin Salman bai tarbi mahaifinsa inda ya sauka daga jirgi ba.

Majiya ya bayyana cewa sarkin da dansa sun samu sabani kan masu zanga-zanga a kasar Algeria, da kuma yadda ake cin zarafin mutanen kasar Yaman.

KU KARANTA: Sai mun kayar da shi: Jam'iyyun siyasa 34, yan takara 20 sun hada kai domin ganin karshen gwamnan jihar Bauchi

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel