Kannywood: Malam Ibrahim Shekarau yayi fitowa ta musamman a fim din Hausa

Kannywood: Malam Ibrahim Shekarau yayi fitowa ta musamman a fim din Hausa

Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma zababben sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau, ya yi wata fitowa ta musamman a wani fim din Hausa mai suna ‘Al’ummarmu’ inda ya yi kira ga kallon finafinan Hausa su rungumi kallon finafinai irin Al’ummarmu, domin karin dankon zumunci tsakanin Musulmi da Kirista.

Wannan bayyanar da wani mashahurin dan siyasa yayi a cikin fim na zaman irin ta ta farko a masana'antar wanda kuma masu sharhi ke ganin hakan zai karfafa masana'antar da kuma hadin kan kasa Najeriya da ta ke da rinjayen mabiya addinan biyu, wato Musulmi da Kirista.

Kannywood: Malam Ibrahim Shekarau yayi fitowa ta musamman a fim din Hausa
Kannywood: Malam Ibrahim Shekarau yayi fitowa ta musamman a fim din Hausa
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Sabbin hotunan Rahama Sadau tana talla

Shi dai wannan fim din an shirya shi ne da nufin kawo hadin kai tsakanin mabiya wadannan addinai, inda fitattun jarumai irin su Ibrahim Maishunku, Al’amin Buhari, Shehu Hassan Kano, Ladidi Tubeless, Ishaq Sidi Ishaq da sauransu su ka jagoranci wakilcin bangarorin biyu.

Majiyar mu mai tushe daga hukumar tace finafinai ta tabbar wa da wakilinmu cewa, da fari an saka wa fim din sunan ‘Arewa’ ne, saboda karfafi gwiwar hadin kai tsakanin Musulmi da Kiristan arewacin kasar, to amma a ka sauya sunan fim din zuwa ‘Al’ummarmu’.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel