Kannywood: Sabbin hotunan Rahama Sadau tana tallar ababen marmari sun tayar da kura

Kannywood: Sabbin hotunan Rahama Sadau tana tallar ababen marmari sun tayar da kura

Fitacciyar jarumar nan a masana'antar shirya fina-finan Hausa watau Kannywood da ma na turanci watau Nollywood, watu Rahama Sadau ta saki wasu sabbin zafafan hotunan ta cikin wani irin salo mai ban sha'awa da ba'a saba gani ba.

Jarumar dai wadda bata da dade da kammala karatun digirin ta ba a kasar Turkiyya, ta saka hotunan ne nata a shafukan ta na sada zumun ta na Facebook, Tuwita da kuma Instagram wadan da kuma ke cigaba da jan hankalin masoyan ta har yanzu.

Kannywood: Sabbin hotunan Rahama Sadau tana tallar ababen marmari sun tayar da kura
Kannywood: Sabbin hotunan Rahama Sadau tana tallar ababen marmari sun tayar da kura
Asali: UGC

KU KARANTA: Kishin-kishin din maganar auren Nafisa Abdullahi ta taso

Legit.ng Hausa ta samu cewa a hotunan nata, an gan ta sanye da kaya irin na turawan yamma, dogon wando kasa-kasa mai dan rodi-rodi da kuma bakar riga itama karama wadda ta dan kame mata jiki sai kuma hula da ta rufe kan ta amma ba hijabi.

Abun da yafi daukar hankali kuma shine yadda ta dauki hotunan da ababen marmari kamar su Tuffa da Fiya a wani irin salo kai kace ma tallar su take yi.

Tuni dai wadannan hotunan suka yi ta daukar hankali a shafukan nata inda masoyan ta da dama suka yaba sannan suka kara yada su suma.

Ga dai hotunan nan:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel