Dole acewa mijin iya baba: Har yau har gobe ni uban gidan Buhari ne - Obasanjo

Dole acewa mijin iya baba: Har yau har gobe ni uban gidan Buhari ne - Obasanjo

- Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa kalubalantar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ke yi ba wai domin kiyayya bane

- Obasanjo ya ce dalilin kalubalntar wannan gwamnati ba zai wuce bunkasa demokaradiyya da bunkasa tattalin arziki da ma ci gaban kasar baki daya

- Ya kara da cewa wadanda ke yi gum da bakinsu a muhallan da babu wani ci gaba to suma suna bayar da gudunmowa wajen habbaar ta'addanci

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa kalubalantar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ke yi ba wai domin kiyayya bane. Ya ce yana kalubalantar gwamnati Buhari saboda har yau har gobe shi ubangidan shugaban kasar ne.

A cewar Obasanjo, "Ina kalubalantar shirye shirye da tsare tsare na gwamnati mai ci a yanzu domin tabbatar da cewa abubuwa na tafiya yadda ya kamata bisa tsari na demokaradiyya."

Ya bayyana hakan a ranar Talata a wani bukin taro na murnar cikarsa shekaru 82 da haihuwa, wanda ya gudana a dakin karatu na Obasanjo da ke garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Jagororin PDP sun mamaye shelkwatar INEC kan zaben shugaban kasa

Dole acewa mijin iya baba: Har yau har gobe ni uban gidan Buhari ne - Obasanjo
Dole acewa mijin iya baba: Har yau har gobe ni uban gidan Buhari ne - Obasanjo
Asali: Twitter

"Buhari; babu wata 'yar tsama tsakanina da shi. Ni ubangidansa ne, idan har da arziki da mutunci. Abun lura a nan shine, na taba kasancewa a irin matsayinsa fiye da dadewar duk wani shugaban da ya mulki kasar.

"Dalilin kalubalntar wannan gwamnati ba zai wuce bunkasa demokaradiyya da bunkasa tattalin arziki da ma ci gaban kasar baki daya.

"Ku gane cewa a cikin demokaradiyya, kalubalantar tsare tsaren gwamnati ba wai harkallar iyalai ba ce; yau ko da ace kanina ko yanana ne ke shugabantar kasar kuma baya aikata komai , ya zamar mun wajibi na kalubalance shi."

Tsohon shugaban kasar ya kara da cewa wadanda ke yi gum da bakinsu a muhallan da babu wani ci gaba to suma suna bayar da gudunmowa wajen habbaar ta'addanci.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel