Mambobin jam’iyyar PDP, ADP, DPN sun sauya sheka zuwa APC a Lagas

Mambobin jam’iyyar PDP, ADP, DPN sun sauya sheka zuwa APC a Lagas

Akalla mutane 700 ne suka sauya sheka daga jam’iyyun Peoples Democratic Party (PDP) da Action Democratic Party (ADP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress(APC) a ranar Talata, 5 ga watan Maris a Lagas.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa masu sauya shekar sun koma APC ne yayin wani kayataccen lyafa da aka shirya a sakatariyar jam’iyyar da ke Ikeja.

Wasu daga cikin sabbin shigar sun hada da Misis Mary Dominance, yar takarar kujerar majalisar wakilai a ADP (Apapa) a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu, da kuma Misis Linda Famoruti, jagorar kungiyar baki mazauna Lagas na PDP.

Mambobin jam’iyyar PDP, ADP, DPN sun sauya sheka zuwa APC a Lagas
Mambobin jam’iyyar PDP, ADP, DPN sun sauya sheka zuwa APC a Lagas
Asali: Facebook

Sauran su hada da Alhaji Abass Obesere, shahararren mawakin fuji, wanda ya sauya sheka tare da mambobin kungiyarsa a PDP, da Mista Adeniyi Abiola, mai aiwatarwa, a kungiyar Articulated Agenda, kungiyar dake goyon bayan dan takaran shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta shafe dukkan tuhume-tuhumen da ake wa marigayi Alex Badeh

Dan takaran kujeran majalisa yankin yammacin Lagas a jam’iyyar Democratic Party of Nigeria (DPN) a zaben da ya gabata, Mista Kayode, ya jagoranci wassu magoya bayan tsohon jam’iyyansa zuwa APC.

Yayinda yake karban bakuncin mambobin, shugaban APC a jihan, Alhaji Tunde Balogun, yace shi da sauran mambobin jam’iyyansa sunyi murnar karban bakuncin su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel