Babbar nasara: Yadda aka gano hanyar magance cutar kanjamau

Babbar nasara: Yadda aka gano hanyar magance cutar kanjamau

- A karo na biyu tun bayan bullar wannan annoba a duniya, rahotanni sun bayyana cewa an samar da warakar cutar kanjamau (H.I.V) da ke jikin wani maras lafiya

- Mamakin wannan nasarar a yanzu da aka samu maganin cutar ta H.I.V ya kara tabbatar da cewa kowacce cuta tana da magani, ma damar za a fadada bincike

- Har yanzu dai ba a bayyana suna ko matsayin maras lafiyar da ya samu waraka ba, kawai dai masana kimiyya na kiransa da 'maras lafiyar Burtaniya'

A karo na biyu tun bayan bullar wannan annoba a duniya, rahotanni sun bayyana cewa an samar da warakar cutar kanjamau (H.I.V) da ke jikin wani maras lafiya, cutar da ke haifar da cutar mai kashe garkuwar dan Adam, AIDS.

Rahoton hakan ya bayyana shekaru 12 bayan da maras lafiya na farko ya samu waraka, lamarin da ya sa masu bincike suka dukufa ainun, amma suka gaza samar da maganin warakar cutar. Mamakin wannan nasarar a yanzu da aka samu maganin cutar ta H.I.V ya kara tabbatar da cewa kowacce cuta tana da magani, ma damar za a fadada bincike.

Masu binciken da suka wallafa rahoton gano maganin cutar a ranar Talata a wata mujalla, tare da kuma gabatar da bayanai a wani taro da aka gudanar kan kwayoyin cututtuka masu wahalar magani da kuma yiyuwar samun maganinsu a garin Seattle.

KARANTA WANNAN: Kwamitin shugaban kasa ya bukaci APC ta gaggauta janye matakin korar Okorocha

Babbar nasara: Yadda aka gano hanyar magance cutar kanjamau
Babbar nasara: Yadda aka gano hanyar magance cutar kanjamau
Asali: UGC

A bayyana, masana kimiyyar sun bayyana lamarin a matsayin wani dogon buri na nan gaba. A zantawarsu da manema labarai, kwararrun sun kira ci gaban a matsayin waraka, da cewar sai sun gano sahihin sunan da ya dace da maganin duk da cewa sun nazarce shi ta fuska biyu ne kawai.

Dr. Wensing shi ne shugaban IciStem, wata kungiyar masana kimiyya na kasashen yamma da ke nazartar kwayoyin halittar da ke iya warkar da cutar kanjamau ta hanyar musanya bargo. Kungiyar na samun tallafi daga AMFAR, cibiyar bincike kan cuta mai karya garkuwar dan Adam da ke Amurka.

Har yanzu dai ba a bayyana suna ko matsayin maras lafiyar da ya samu waraka ba, kawai dai masana kimiyya na kiransa da "maras lafiyar Burtaniya".

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel