La'anannun Allah: Yadda rigimar kudi ta ja aka kama wasu 'yan luwadi a Katsina

La'anannun Allah: Yadda rigimar kudi ta ja aka kama wasu 'yan luwadi a Katsina

Jami'an rundunar yan sandan Najeriya a jihar Katsina ta sanar da samun nasarar cafke wani mutum mai suna Aminu Mai Unguwa Tsanni, mai shekaru 45 bisa laifin yin luwadi da wasu mutane biyu ba tare da ya biya su kudin da suka shirya ba, a hotel din Katsina.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Katsina DSP Gambo Isa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a jihar ta Katsina inda yace, Aminu Mai Unguwa Tsanni, ana tuhumar sa da laifin yin luwadi da Abdullahi Abubakar, mai shekaru 20 da kuma Rabi’u Yahuza, mai shekaru 23 dukkan su a garin Katsina da laifin na luwadi.

La'anannun Allah: Yadda rigimar kudi ta ja an kama wasu 'yan luwadi a Katsina
La'anannun Allah: Yadda rigimar kudi ta ja an kama wasu 'yan luwadi a Katsina
Asali: UGC

KU KARANTA: Malamin addinin da ya yi hasashen faduwar Buhari ya sake magana

Legit.ng Hausa cewa an sami nasarar damke su ne, bayan wanda ake zargi da luwadin da su, ya gaza biyan su kudin alkawarin da ya yi masu na naira dubu goma-goma kowannensu, amma da ya gama biyan bukatarsa da su sai ya gudu ba tare da ya basu ko sisin kwabo ba, inda su kuma suka yi awon gaba da wayoyin hannunsa har guda biyu.

Wannan ne ya harzuka Mai Ungwa Tsanni, inda ya yi karar mutanen biyu a ofishin yan sanda dake Sabon Gari cikin birnin Katsina, bisa zarginsu da sace masa wayoyin hannunsa.

Da binciken yan sanda ya tsananta sun gano cewa, akwai lauje cikin madi game da satar da akai masa, akwai alamun cewa lalata ya yi da su bai biya ba.

Tuni yan sandan suka maka su a gaban kuliya manta sabo domin ci gaba da gano yadda ba'asin ya kasance, domin yi masu hukuncin da ya dace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel