Yadda karamar hukumar cikin garin maiduguri ta tarawa Buhari kuri'u mafi yawa a Nigeria

Yadda karamar hukumar cikin garin maiduguri ta tarawa Buhari kuri'u mafi yawa a Nigeria

Karamar hukumar cikin garin Maiduguri da ke jihar Borno, ta zamo karamar hukumar da ta fi kowacce karamar hukuma a Nigeria tarawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabreru.

Sakamakon zaben da aka kad'a ya nuna cewa karamar hukumar cikin garin Maiduguri ta tarawa shugaban kasa Buhari kuri'u 146,181, wanda ya bata damar doke sauran kananan hukumomi 774 da ke tarayyar Nigeria da suka tarawa Buhari kuri'un da ya bashi damar zarcewa a karo na biyu.

A hannu daya kuwa, karamar hukumar Zaria, ta kasance mai bi wa karamar hukumar cikin garin Maiduguri, inda ta baiwa shugaban kasar kuri'u 111,082, wanda har ya sanya gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya sa masu albarka bisa gagarumar goyon bayan da suka baiwa shugaban kasar.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Kungiyar JUSUN ta garkame babban alkalin jihar Nasarawa a ofishinsa

Yadda karamar hukumar cikin garin maiduguri ta tarawa Buhari kuri'u mafi yawa a Nigeria
Yadda karamar hukumar cikin garin maiduguri ta tarawa Buhari kuri'u mafi yawa a Nigeria
Asali: UGC

Sai dai, mazauna garin Zaria ba su yi mamaki akan wannan nasara da Buharin ya samu ba, da kuma kasancewarsu na biyu a sahun kananan hukumomin da suka fi tarawa Buhari kuri'u kasancewar garin ya kasance tare da Buhari tun a siyasarsa ta 2003.

Daya daga cikin mazauna garin, Yunus Ahmad, ya ce yawan kuri'un da ya zarce hakan idan da ace kashi 70 na masu kad'a kuri'a sun fito sun yi zabe a waccan rana.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel