A karshe: Mun gano wadanda ke haddasa rikicin jihar Benue - Rundunar soji

A karshe: Mun gano wadanda ke haddasa rikicin jihar Benue - Rundunar soji

- Rundunar soji ta ce ta gano yadda wasu masu madafun iko a jihar benue ke haddasa rikici da daukar nauyin hare haren da ake kaiwa al'ummomin jihar

- Rundunar ta ce hakan ba zai zo da mamaki ba, la'akari da irin harin da aka kai garin Agatu ana mako daya zaben shugaban kasa, da harin Yammacin garin Gwer

- Ta ce rundunar ta fadada ayyukanta a kan titin Loko zuwa Agatu, Kwande da kuma iyakar garuruwan Benue domin dakile hare hare a nan gaba

Rundunar soji ta ce ta gano yadda wasu masu madafun iko a jihar benue ke haddasa rikici da daukar nauyin hare haren da ake kaiwa al'ummomin jihar. Manjo Janar Adeyemi Yekini, kwamandar rundunar na atisayen 'Whirl Stroke (OPWS)', ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya karanta a yayin taron manema labarai a Makurdi.

Yekini ya kuma ce ire-iren wadannan masu madafun ikon, su ne ke kara rura rikici a garuruwan kamar yadda aka gani a lokutan baya, kan irin hare haren da ake kaiwa jihar gabanin babban zaben kasar.

KARANTA WANNAN: PDP ba ta isa ta hana mu bin umurnin Buhari ba - Rundunar soji ta yiwa Atiku martani

A karshe: Mun gano wadanda ke haddasa rikicin jihar Benue - Rundunar soji
A karshe: Mun gano wadanda ke haddasa rikicin jihar Benue - Rundunar soji
Asali: Depositphotos

"Abun takaici ne matuka yadda wasu masu madafun iko ke haddasa rikici a jihar Benue; Hakan ba zai zo da mamaki ba, la'akari da irin harin da aka kai garin Agatu ana mako daya da zaben shugaban kasa, yanzu kuma an sake kai wani harin a Yammacin garin Gwer, ana saura mako daya zaben gwamnoni."

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya ruwaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da atisayen OPWS a shekarar 2018 domin dakile matsalar tsaro musamman satar shanu, garkuwa da mutane, da kuma tashin hankula a jihohin Benue, Nasarawa da Taraba.

Kwamandan rundunar ya ce rundunar ta fadada ayyukanta a kan titin Loko zuwa Agatu, Kwande da kuma iyakar garuruwan Benue domin dakile faruwar kai hare hare a garuruwan a nan gaba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel