Assha: An kama mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa a otal da matar aure

Assha: An kama mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa a otal da matar aure

Wani hoton bidiyo da ke zaga gari, wanda ke nuna mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa kuma zababben sanatan mazabar jihar Nasarawa ta arewa, Godiya Akwashiki, tumbur haihuwar uwarsa na ci gaba da haddasa ce-ce-ku-ce a tsakanin al'umma.

Daya daga cikin bidiyoyi biyar da ke zagawa, mai tsawon sakan goma sha shida na nuna dan siyasar ne tumbur haihuwar uwarsa, inda wasu mutum biyu ke ci gaba da cin zarafinsa ba kakkautawa.

Bidiyo na biyu kuma na nuna Sanata Akwashiki ne zaune a cikin motarsa daga shi sai 'yar karamar rigar ciki, ita ma a yayyage. Sai bidiyo na uku kuma ya nuna shi tumbur kwance a kasa da alamun an tuburbuda shi.

A wani bidiyon kuma, an hango Akwashiki ne kwance a kan gadon asibiti, inda wasu mutum biyu ke zaune a kusa da shi suna jinyarsa.

Bidiyoyin na nuna yadda wasu mutum biyu ke lallasa Sanata Godiya Akwashiki bayan sun tube shi zindir, inda shi kuma ke ta rokon afuwa.

An zargi cewa dalilin lallasa Sanata Akwashiki a cikin bidiyon, na da nasaba da kama shi da aka yi a dakin otal da wata matar aure yana lalata da ita. Kodayake dai ba a nuna matar a bidiyon ba.

KU KARANTA: Dan Allah kuyi hakuri, sarki gargajiya a Rivers ya roki hukumar Soji kan kisan Sojoji biyu a garin

Kakakin 'yan sandan birnin tarayya Abuja, Anjuri Manzah, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya bayyana cewa Akwashiki baya hannunsu, amma suna gudanar da bincike akan lamarin.

"Muna aiwatar da bincike akan lamarin," inji kakakin 'yan sandan.

Gwamnatin jihar Nasarawa ta kira wani taron gaggawa a ranar Asabar din da ta gabata don tattauna babutuwa akan bullar bidiyon.

Duk wani kokari da manema labarai suka yi don su ji ta bakin Sanata Akwashiki ya ci tura sakamakon rashin shiga da wayarsa ke yi.

Shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, Philip Tatari Shekwo, a wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi, ya bayyana rashin jin dadin jam'iyyar APC bisa bullar bidiyon.

Shugaban ya yi Allah wadai da cin zarafin da aka yi wa Sanata Akwashika, inda ya ce, "Abin takaici ne irin cin mutuncin da aka yi ga babban mutum irin wannan ko da kuwa zargin da a ke yi masa gaskiya ne."

Ya ci gaba da cewa, jam'iyyar APC a matakin jiha ta kafa wani kwamiti da zai yi bincike akan lamarin don gano gaskiyar abinda ya faru.

A cewar shugaban na APC reshen jihar Nasarawa, "Duk wanda muka samu da hannu a lamarin kuma in har dan jam'iyyar mu ne, to jam'iyya a matakin jiha za ta hukunta shi daidai da tanadin dokar jam'iyya, kamar dai yadda APC din za ta bari dokar kasa ta yi aiki akan wadan da suka aikta danyen aikin."

"Muna kira ga duk wanda wannan lamari ya shafa da su yi hakuri, har zuwa lokacin da za mu kammala bincike."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel