Ba gudu ba ja da baya: Ni cikakken dan PDP ne, ba zan koma APC ba - Dino Melaye

Ba gudu ba ja da baya: Ni cikakken dan PDP ne, ba zan koma APC ba - Dino Melaye

- Sanata Dino Melaye ya yi fatali da labarin da ake yadawa na cewar yana shirin ficewa daga jam'iyyar PDP domin komawa jam'iyyar APC

- Dino Melaye ya ce ba zai iya ficewa daga jam'iyyar PDP ba wacce a karkashinta ne al'ummar Kogi ta Yamma suka zabe shi a karo na biyu

- Ya kuma jaddada cewa ba zai iya komawa APC ba, wacce a cikin shekaru ukku da rabi ta lalata duk wani ci gaba na jihar Kogi, wanda ya jawo silar asarar rayuka da dama

Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta Yamma, Sanata Dino Melaye ya yi fatali da labarin da ake yadawa na cewar yana shirin ficewa daga jam'iyyar adawa ta PDP domin komawa jam'iyya mai mulki ta APC.

Melaye wanda aka zabe shi a ranar Asabar da ta gabata domin komawa kujerarsa a karo na biyu, ya ce ya zama wajibi ya karyata wannan jita-jitar saboda ganin cewa "babu kamshin gaskiya ko abun da hankali zai dauka a ciki, duba da cewa ya tsaya takara a jam'iyyar adawa ta PDP kuma al'ummar mazabar Kogi ta yamma suka zabe shi inda ya lallasa wadanda suke ganin suna da madafun iko."

A cikin wata sanarwa da ya bayar a ranar Juma'a ta hannun mai tallafa mashi ta fuskar watsa labarai, Gideon Ayodele, Mr Melaye ya ce labarin abun dariya ne, wai ace zai iya shiga jam'iyyar da cikin shekaru ukku da rabi ta lalata duk wani ci gaba na jihar Kogi, wanda ya yi nuni da cewa ya jawo silar asarar rayuka da dama.

KARANTA WANNAN: Assha: Mutane 32 sun mutu a wani sabon hari da 'yan ta'adda suka kai Zamfara

Ba gudu ba ja da baya: Ni cikakken dan PDP ne, ba zan koma APC ba - Dino Melaye
Ba gudu ba ja da baya: Ni cikakken dan PDP ne, ba zan koma APC ba - Dino Melaye
Asali: Depositphotos

"Muna so mu bayyana maku karara cewa babu hadi tsakanin duhu da haske, ko tsakanin wuta da auduga. Ni sanata Dino Melaye na tsaya a bangaren haske, ita kuwa gwamnatin APC mai mulki a jihar Kogi ita ce ke cikin duhu.

"Sai dai, jita jitarsu ta kara nuna irin matsayi da darajar da Sanata Dino Melaye ya ke da ita a cikin jihar Kogi dama siyasar Nigeria ba ki daya. Ya zama wajibi kowa ya sani cewa wannan jita-jitar ba gaskiya ba ce, kamar labarin kanzon kurege ne," a cewar sanarwar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel