Asiri ya tonu: Ya shekara 20 yana tuka jirgin sama da takardun boge

Asiri ya tonu: Ya shekara 20 yana tuka jirgin sama da takardun boge

An shiga rudani mai tsanani a kasar Afrika ta kudu biyo bayan labarin gano wani matukin jirgin sama mai suna William Chandler da ya kwararre kuma ya shafe sama da shekaru 20 yana tuki da takardun shaidar bogi.

Kamar dai yadda majiyar mu ta sanar mana, matukin jirgin ya soma aiki ne da kamfanin sufurin jiragen saman kasar na South African Airways kimanin shekaru 20 da suka wuce sai dai wani bincike ne da aka gudanar yanzu ya fallasa bahallatsar ta sa.

Tashin hankali: Ya shekara 20 yana tukin jirgin sama da takardun boge
Tashin hankali: Ya shekara 20 yana tukin jirgin sama da takardun boge
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Cacar baki ta shiga tsakanin Okorocha da Oshiomhole

Majiyar mu ta Eyewitness News dai ta labarta mana cewa tuni dai wannan sakamakon binciken ya tilastawa mutumin yin murabus din dole daga kamafanin tare da bada hakuri.

Da suke maida bahasi game da hakan, su kuwa mahukunta a ma'aikatar sufurin kasar sun bayyana cewa tuni suka soma wani yunkurin ganin sun kwalkwalo dukkan kudaden albashin da suka biyashi tsawon shekaru.

Sai dai labarin na mutumin ya tayar da hankalin mutanen kasar sosai inda suka soma nuna shakku akan shiga jiragen kasar musamman ma mallakin kamfanin sufurin kasar domin a cewar su ba su san wanda zai tuka su ba ko ya kware ko kuwa a'a.

Ga dai mutumin nan da matar sa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

KAith a letter, digits, period, question or exclamation mark, closing quote or bracket.

Asali: Legit.ng

Online view pixel