Bata kare ba: Duk da Buhari ya lashe zabe, za'a sake zaben shugaban kasa a jihohi uku - INEC

Bata kare ba: Duk da Buhari ya lashe zabe, za'a sake zaben shugaban kasa a jihohi uku - INEC

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wto INEC ta bayyana cewa ta zabi ranar 9 ga watan Maris matsayin ranar sake gudanar da zaben shugaban kasa a wasu wuraren da aka samu matsala a ranar Asabar, 23 ga watan Febrairu, 2019.

Kwamishanan labarai na hukumar INEC, Festus Okoye, ya bayyana cewa za'a gudanar da zaben ne tare da zaben gwamnoni da majalisar dokokin tarayya.

Okoye ya ce an yanke wannan shawara ne bayan ganawar hukumar da wakilan INEC dake jihohin tarayya a ranar Alhamis, 28 ga watan Febrairu, 2019.

KU KARANTA: Manyan kasashen duniya 10 sun taya Buhari da 'yan Nigeria murna

INEC ta yi watsi da zaben wasu wurare sakamakon rikice-rikice wanda ya hana hukumar aika kayan zabe da ma'aikata wajen domin kare rayukansu.

Wadannan wurare sun kunshi kananan hukumomi biyu a jihar Ribas, jihar Legas da jihar Anambara.

Jawabin yace: "Saboda haka, hukumar ta yanke shawara cewa za'a gudanar da zaben a dukkan wuraren da ba'a samu daman gudanar da zabe ba a ranan Asabar, 9 ga watan Maris tare da zaben gwamnoni da yan majalisun dokokin jiha,".

Za ku tuna cewa rikice-rikice a unguwar Okota dake jihar Legas ya sanda INEC tayi watsi da sakamakon zaben wajen, kana kashe-kashe da aka yi a jihar RIbas inda akalla mutane 20 suka rasa rayukansu ranar zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel